2027: Tsohon Gwamnan Ebonyi Zai Jagoranci Kwamitin Tantance Masu Neman Takara a NDC

2027: Tsohon Gwamnan Ebonyi Zai Jagoranci Kwamitin Tantance Masu Neman Takara a NDC

  • Jam'iyyar NDC ta kafa kwamitin da zai tantance masu neman takarar shugaban kasa, gwamnoni da 'yan Majalisa karkashin inuwarta a zaben 2027
  • Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sanata Sam Egwu, shi ne zai jagoranci wannan kwamiti, mai kunshe da mambobi 17
  • NDC ta ce kwamitin ya hada shugabanni, kwararru da kuma mambobin kwamitin gudanarwa da aka zabo domin kula da aikin tantance ‘yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NDC ta fara shirye-shiryen tantance yan siyasar da suka nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da yan Majalisar wakilai a 2027.

NDC ta nada tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sanata Sam Egwu, a matsayin shugaban kwamitin tantance masu neman takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da ‘yan majalisar wakilai gabanin zaben 2027.

Sam Egwu.
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sam Egwu a wurin ajiyar motoci tare da dogarinsa Hoto: Sam Egwu
Source: Facebook

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakatarenta na kasa, Ikenna Morgan Enekweizu, ya fitar ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanata Goje ya sha kaye, ya rasa tikitin APC na komawa Majalisar Dattawa a 2027

Sanarwar ta ce za a kaddamar da kwamitin mai mutum 17 da karfe 4:00 na yammacin ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026.

Sam Egwu zai jagoranci tantance ‘yan takara

Egwu, wanda ya taba zama gwamna sau biyu a jihar Ebonyi, sannan kuma tsohon dan majalisa, zai jagoranci aikin tantance masu neman mukaman siyasa karkashin jam’iyyar NDC.

Jam’iyyar ta kuma nada mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na kasa, Reuben Egwuaba, a matsayin sakataren kwamitin.

Sunayen sauran mambobin kwamitin

Sauran mambobin kwamitin sun hada da:

1. Babatunde Ali — mataimakin shugaban kwamitin

2. Buba Galadima

3. Mohammed Takori

4. Daniel Onifade

5. Ikeddy Isiguzo

6. Wole Adedayo

7. Dr Osusu Osusu

8. Chief Asukewe Ikoawaji

9. Prof. Udenta Udenta

10. Frederick E. Owotorufa

11. Hannatu Tanko

12. Dogo Shammar

13. Sir Henry Obaze

14. Clement Agiagie

15. Fatima Abba.

Taron NDC.
Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wurin babban taron NDC na kasa Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

Jam’iyyar ta ce kwamitin ya kunshi shugabannin jam’iyya, kwararru da kuma mambobin kwamitin gudanarwa na kasa da aka zabo domin kula da aikin tantance ‘yan takara a zaben 2027.

NDC ta fara shirye-shiryen zaben 2027

Kara karanta wannan

APC: Akpabio, Barau Jibrin da gwamnoni 7 za su fafata a neman takarar sanata yau

Matakin na zuwa ne yayin da NDC ta kara zage damtse wajen shirye-shiryenta da nufin tunkarar babban zaben 2027, cewar rahoton Vanguard

A baya-bayan nan jam'iyyar NDC ta fara amfani da tsarin masalaha wajen zaben fidda gwani a wasu yankuna domin kauce wa rikice-rikicen cikin gida da kuma karfafa hadin kan jam’iyyar.

NDC ta rufe sayar da fam din takara

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar hamayya ta NDC ta rufe sayar da fam na neman takarar shugaban ƙasa na babban zaben 2027.

Bayanai daga jam'iyyar sun tabbatar da cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ne kaɗai.ya sayi fam ɗin.

Jam’iyyar ta ce ta ƙara wa’adin karɓar fam ɗin nuna sha’awa na gwamnoni, sanatoci da yan Majalisar dokoki ta tarayya da ta jihohi da mako guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262