Rigima Ta Barke a Kaduna, Zaben Fitar da Gwani Ya Jefa Shugaban APC a Matsala

Rigima Ta Barke a Kaduna, Zaben Fitar da Gwani Ya Jefa Shugaban APC a Matsala

  • Jam’iyyar APC ta shiga rikici a Igabi bayan fusatattun matasa sun nuna rashin amincewa game da zaben fitar da gwani a Kaduna
  • Matasan sun tilasta shugaban jam’iyyar Bashir Jibrin Jaji shiga mota saboda zargin magudin zaɓe
  • Sun ce ba a yi tantance masu kaɗa ƙuri’a ko ƙirga ba kafin jami’an jam’iyya su bayyana Hussaini Jalo a matsayin wanda ya yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Igabi, Kaduna - An ɗauke shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna, Bashir Jibrin Jaji.

Hakan ya biyo bayan fusatar matasa da ke nuna rashin gamsuwa da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC na kujerar majalisar wakilai da aka gudanar.

Zaben fitar da gwani a Kaduna ya koma rikici
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Source: Twitter

Kaduna: Zargin da matasan APC ke yi

Lamarin ya faru ne bayan matasan sun zargi shugabannin jam’iyya da wasu jami’ai da yin magudi a zaɓen fidda gwani na mazabar Igabi ta tarayya, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hayatudeen: "Matakin da zan dauka kan 'yan bindiga idan na zama shugaban kasa"

An fafata ne tsakanin masu neman takara a jam'iyyar tsakanin Sani Abdulkadir Dakaci da Hussaini Jalo.

Wasu daga cikin matasan sun ce ba a gudanar da tantance masu zaɓe ko ƙirga ƙuri’u yadda ya kamata ba yayin gudanar da zaɓen.

Sun yi zargin cewa jami’an jam’iyya sun fito ba zato ba tsammani suka sanar da Hussaini Jalo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A cewar shaidu, lamarin ya fusata magoya bayan jam’iyyar da dama, inda suka mamaye ofishin APC da ke Rigachikun suka tunkari shugaban jam’iyyar.

Wasu bayanai da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka tilasta shugaban APC na Igabi shiga wata mota bayan rikicin zaɓen fitar da gwanin.

Ɗaya daga cikin mambobin jam’iyyar da ya halarci wurin, Musa Salihu, ya ce magoya baya sun yi layi domin zaɓen amma ba a ƙirga su ba kafin sanar da sakamako.

Ya ce:

“Mun yi layi amma babu wanda ya ƙirga mu. Sai kawai suka fito suka sanar da cewa Jalo ne ya yi nasara. Wannan ba dimokuraɗiyya ba ce.”

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban a INEC ya samu tikiti, zai tsaya takarar gwamnan Yobe a ADC

An samu rigingimu a zaben fitar da gwanin APC
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Abin da masu zabe ke cewa a Kaduna

Wani magoyin bayan jam’iyyar, Musbahu Idris, shi ma ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da tsarin zaɓen a yankin.

Ya ce jam’iyyar ta umarce su su je cibiyar tattara ƙuri’u domin zaɓen, inda mutane suka taru tun ƙarfe shida na safe suna jiran tantancewa.

Ya ƙara da cewa sun yi mamakin jin an bayyana Jalo a matsayin wanda ya yi nasara alhali babu zaɓen da aka gudanar a wurin, cewar Daily Post.

Sai dai wani magoyin bayan shugaban APC, Haruna Sani, ya kare tsarin zaɓen yana cewa an gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani kuma Jalo ya yi nasara.

Haruna ya ce matasan sun rinjaye su sannan suka kai wa shugaban jam’iyyar hari kafin daga bisani su tafi da shi cikin mota.

Abin al'ajabin Zazzau ya janye daga takara

A baya, an ji cewa Mahmud Sadis Buba da ke neman samun takarar dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna ya janye daga neman kujerar a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Hankalin Wike ya tashi da gwamnan Oyo ya fito zai kara da Tinubu a 2027

Dan siyasar da aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye daga takarar a mazabar Sabon Gari karkashin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Ya ce matakin ya biyo bayan kokarin sulhu daga shugabannin APC, bayan tuntuba da iyali, abokan siyasa da masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.