Abu Ya Girma: An Kai Karar Sheikh Jingir gaban Sarkin Musulmi da Shugaba Tinubu
- Femi Fani-Kayode ya sako sarkin Musulmi da Shugaba Bola Tinubu kan kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi
- Tsohon Ministan ya ce kalaman malamin addinin sun jawo damuwa tsakanin al'ummar Kiristoci da Musulmai a Najeriya
- Fani-Kayode ya yabawa Sarkin Musulmi kan kiran da ya yi na a daina cin mutuncin juna tsakanin mabiya addinai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Chief Femi Fani-Kayode, ya mika bukatarsa ga Sarkin Musulmi da Shugaba Bola Tinubu kan kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Femi Fani Kayode ya bukaci Muhammadu Sa'ad Abubakar III da Shugaba Bola Ahmed Tinubu su fito fili su gargadi Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalaman da ya yi.

Source: Facebook
Femi Fani-Kayode ya yi wannan kira ne a cikin wata doguwar sanarwa mai taken 'The Gospel According to Sheik Jingir', wadda ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
"Ba Tinubu na ke tallatawa ba"; Sheikh Jingir ya fadi dalilin tallata muslim muslim
Me Femi Fani Kayode ya ce kan kalaman Jingir?
Ya bayyana damuwarsa kan illar da kalaman da ya kira masu tayar da hankali kan addini za su iya haifarwa.
Tsohon ministan ya ce abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne rahoton da ya ce Jingir ya bayyana cewa bai yi nadamar kalaman da ake zargin ya yi a wani taron jama'a na baya-bayan nan ba.
Ya ce kalaman sun jawo martani mai karfi daga Kiristoci da Musulmi, yana mai cewa ya tattauna da wasu gwamnonin jihohin Arewa Musulmai da kuma wani fitaccen malamin addinin Musulunci, wadanda a cewarsa su ma suka nuna damuwa kan kalaman.
Fani-Kayode ya yabawa Sultan
Fani-Kayode ya yabawa Sultan na Sokoto kan kiran da ya yi a baya-bayan nan ga Kiristoci da Musulmi da su daina cin mutuncin juna, yana mai bayyana matakin a matsayin nasiha ta uba da ta taimaka wajen kwantar da tarzoma.

Kara karanta wannan
"Kiristanci na cikin matsala"; Malamin addini ya dauki zafi kan kalaman Sheikh Jingir
“Ina matukar girmama Sultan na Sokoto tare da kaunarsa sosai, wanda shi ne jagoran al'ummar Musulmi a Najeriya, kuma ya bukaci Kiristoci da Musulmi da kada su rika cin mutuncin juna kwanaki kadan da suka gabata a wani taron tsaro a Abuja,” in ji Fani-Kayode.
Ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su bari bambancin addini ya lalata hadin kan kasar ba, yana mai jaddada cewa Kiristoci da Musulmi duk sun cancanci girmamawa daidai.
Fani-Kayode ya ce matsayinsa ba ya da alaka da kiyayya ga Musulunci, yana mai cewa a kodayaushe yana adawa da duk wani yunkuri na mabiya daya daga cikin addinan biyu na wulakanta dayan.
“Ba na girmama duk wani Kirista da ke neman wulakanta, bata suna da rashin girmama Musulunci, kamar yadda ba na girmama duk wani Musulmi da ke neman yin hakan ga Kiristanci,” in ji shi.
Kiran a dauki mataki
Daga bisani, Fani-Kayode ya yi kira kai tsaye ga Sultan da Shugaba Tinubu da su sanya baki a cikin lamarin.
“Ina kira ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Shugaban kasarmu da muke kauna, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da su fito fili su gargade shi kafin lokaci ya kure,” in ji shi.
Ya ce bai kamata a kalli batun kawai ta fuskar siyasar jam'iyyu ba, yana mai cewa kare zaman lafiya da hadin kan kasa ya fi komai muhimmanci.

Source: Twitter
Sheikh Jingir ya yi karin haske
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin haske kan kalamansa da suka jawo cece-kuce.
Sheikh Jingir ya nesanta kungiyar Izala daga kalaman da ya yi na kira ga ’yan Najeriya su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa na 2027.
Asali: Legit.ng
