Wata Sabuwa: Iran Ta Dura kan Faransa bayan Yaki da Amurka Ya Dan Lafa
- Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya caccaki Faransa kan sukar da ta yi wa Iran game da yanke hukuncin kisa
- Araqchi ya ce Faransa ba ta da hurumin yi wa wasu ƙasashe gargadi kan haƙƙin bil Adama da dokokin ƙasa da ƙasa
- Ya ce goyon bayan Faransa ga Isra’ila a Gaza da matakan da ta ɗauka kan Iran sun rusa ikirarin Paris na kasancewa mai kare haƙƙin bil Adama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya caccaki Faransa kan sukar da ta yi wa Iran game da amfani da hukuncin kisa.
Araqchi ya yi martanin ne bayan Faransa da wasu ƙasashe 25 tare da jami’ar kula da manufofin harkokin wajen Tarayyar Turai, Kaja Kallas, sun yi Allah-wadai da hukuncin kisan da Iran ke aiwatarwa.

Source: Getty Images
Araqchi ya caccaki Faransa
Tashar labaran Tasnim ta ce Araqchi ya yi watsi da yunƙurin Faransa na gabatar da kanta a matsayin mai kare haƙƙin bil Adama.
Ya ce goyon bayan Paris ga hare-haren Isra’ila a Gaza da kuma abin da ya kira ta’asar da aka kai wa Iran ya rusa ikirarin Faransa na samun damar yin wani bayani.
Ya bayyana cewa:
"Ya kamata ƙasashe irin Faransa su daina wa duniya wa'azin 'haƙƙin bil Adama' da dokokin ƙasa da ƙasa. Munafuncin a bayyane yake kuma abin kunya ne."
Iran ta zargi Faransa kan Isra'ila
Araqchi ya ce goyon bayan Faransa ga Isra’ila ya sanya ta rasa damar yin wa Iran ko wasu ƙasashe suka kan batun haƙƙin bil Adama.
Ya ƙara da cewa:
"Goyon bayanku ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma hare-haren da aka kai wa Iran ya rusa duk wani matsayin da kuke ganin kuna da shi."
Ministan ya ce irin wannan matsaya ta nuna abin da Iran ke kira da nuna fuska biyu wajen mu'amala da batutuwan haƙƙin bil Adama.
Zargin da Faransa ta yi
Martanin Araqchi ya biyo bayan wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar tare da wasu ƙasashe 25 da Kaja Kallas ta yi.
Middle East Eye ta wallafa cewa kasashen sun yi Allah-wadai da abin da suka kira ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga a Iran.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin Iran da ta dakatar da amfani da hukuncin kisa tare da sakin mutanen da suka ce ana tsare da su ba bisa ƙa'ida ba.

Source: Getty Images
Matsayar Iran kan kasashen Turai
Tehran ta sha bayyana cewa gwamnatocin ƙasashen Yamma ba za su iya yin wa wasu ƙasashe wa'azi kan dokokin ƙasa da ƙasa ba yayin da suke goyon bayan Isra’ila.
Iran ta kuma zargi ƙasashen Yamma da gaza ɗaukar matakan da suka dace kan ayyukan Isra’ila a Gaza da kuma goyon bayan hare-haren da aka kai mata.

Kara karanta wannan
Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka
Iran ta sauya dabarun kai hari
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta sauya dabarun kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya yayin da yaƙin Amurka da Iran ke ci gaba.
Rahotanni sun ce Iran ta yi amfani da jirage ƙanana marasa matuƙa da makamai masu linzami wajen kai hare-hare kan sansanonin Amurka guda uku da ke Jordan cikin kwanaki biyar a watan Yuni.
An ce dakarun IRGC sun yi amfani da wasu makamai masu linzami da za su iya sauya alkibla kwatsam, lamarin da ya tilasta wa Amurka amfani da makamai masu kariya na Patriot da ke da ƙarancin adadi.
Asali: Legit.ng

