2027: Amaechi Ya Sanar da ADC dan Takarar da Zai Kifar da Tinubu

2027: Amaechi Ya Sanar da ADC dan Takarar da Zai Kifar da Tinubu

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa domin zabar sababbin shugabanni
  • Tsohon Ministan sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya yi jawabi a wajen taron
  • Rotimi Amaechi ya sanar da jam'iyyar ADC dan takarar da za ta tsayar wanda zai iya kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Chibuike Amaechi, ya ba jam'iyyar ADC shawara kan zaben shugaban kasa na 2027.

Amaechi ya buƙaci jam’iyyar ADC da ta zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa mai inganci wanda zai iya lallasa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Amaechi ya ba jam'iyyar ADC shawara
Rotimi Amaechi da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a babban taron jam’iyyar ADC na ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Wace shawara Rotimi Amaechi ya ba ADC?

Amaechi ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji la’akari da ƙabila ko addini yayin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa irin wannan mataki zai iya gurgunta ƙoƙarin gina gagarumar haɗaka, tashar Arise News ta kawo rahoton.

“Idan kuna tunanin shugaba Tinubu zai mika muku mulki, kuna ɓata lokacin ku ne. Dole ne ADC su taru su yanke shawara kan ɗan takara mai inganci."
“Lokacin da muka shiga APC [kafin 2015], mun nemi ɗan takara mai inganci, kuma mun yi nasara. Ƙabila da addini za su mayar da mu baya ne kawai zuwa inda muka fara.”

- Rotimi Chibuike Amaechi

Amaechi ya soki gwamnatin Tinubu

Amaechi ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan zargin murƙushe ’yan adawa.

A ranar Litinin, jam’iyyar ADC ta ce an hana ta damar yin amfani da dandalin Eagle Square da kuma babban filin wasa na Moshood Abiola National Stadium domin gudanar da babban taron nata.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Ko gawa aka tsayar, za ta buga Tinubu da kasa a zaben 2027'

Daga baya jam’iyyar adawar ta sanar da zauren taro na Rainbow event centre da ke Abuja a matsayin wurin da za a gudanar da taron.

Amaechi ya ba ADC shawara
Rotimi Amaechi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter
“Me ya sa jami’in gwamnati zai yi ƙoƙarin hana mutane haƙƙinsu da ke cikin kundin tsarin mulki na 'yancin yin taro?"
“Ya mutumin da [Tinubu] ke iƙirarin cewa shi ɗan dimokuradiyya ne kuma ya taɓa kasancewa tare da NADECO, yanzu yake aikata abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idodin dimokuradiyya? Idan har abin da suka tsaya a kansa ke nan, to wannan ya kai matsayin ƙoƙarin hukunta ’yan Najeriya.”

- Rotimi Chibuike Amaechi

'Yan bindiga sun farmaki Amaechi

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun farmaki tawagar motocin tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Rotimi Amaechi, ya bukaci hukumomin tsaro su kamo ƴan bindigar da suka farmaki ayarin motocinsa tare da ƙona ofishin jam’iyyar ADC a garin Ubima.

Maharan sun ƙona ofishin jam'iyyar ADC na mazabar Ubima, sannan suka yi ta harbe-harbe tare da yin kaca-kaca da ƙofar gidan iyayen Amaechi da harbin bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng