"Ba Gaskiya ba ne," Tsagin Kwankwaso Ya Maida Martani ga Shugaban Jam'iyyar PRP

"Ba Gaskiya ba ne," Tsagin Kwankwaso Ya Maida Martani ga Shugaban Jam'iyyar PRP

  • Shugaban PRP ya ce Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso sun bukaci tikitin takarar shugaban kasa kafin shiga jam’iyyar
  • Kungiyar Kwankwasiyya ta musanta zargin, ta ce Baba-Ahmed na neman daukar hankali ne kawai amma ba gaskiya ya fada ba
  • Ta bayyana cewa PRP ce da kanta ta roki Kwankwaso da Obi su shigo jam'iyyar amma babu wani zama da aka yi kan wannan batu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban jam’iyyar PRP, Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana cewa jagororin adawa, Peter Obi, da Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi kokarin shiga PRP amma hakan ba ta yiwu ba.

Baba Ahmed ya ce jiga-jigan biyu sun nemi a ba su tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye ba tare da hamayya, lamarin da ya ce PRP ba ta yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Kafin su koma NDC, Kwankwaso da Peter Obi sun yi yunkurin shiga jam'iyyar PRP

Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a taron yan Kwankwasiyya a Kano Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Tsagin Rabiu Kwankwaso ya yi martani

Sai dai kungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da kalaman shugaban PRP, tana mai cewa yana neman daukar hankali ne kawai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Mai magana da yawun kungiyar, Habeeb Saleh Mohammed, ya ce shi bai san da wata tattaunawa da Kwankwaso ko Peter Obi suka bukaci tikitin shugaban kasa daga PRP ba.

“A gaskiya duk wanda ya san yadda lamarin yake zai tuna cewa PRP ce ta fito a talabijin ta bakin shugabanta Hakeem Baba-Ahmed tana kira ga Peter Obi da jagorana da sauran ‘yan hadaka su shiga jam’iyyar,” in ji shi.

Ya ce baya ga irin wannan kira da aka yi a bainar jama’a, bai san da wani zama a hukumance da aka yi inda aka gabatar da irin wadannan bukatu ba.

Kwankwaso da Obi sun nemi tikitin PRP?

Habeeb Mohammed ya ce:

“Ban san wani zama da aka yi tsakanin jagorana, Peter Obi da PRP inda suka bukaci a ba su tikitin shugaban kasa kai tsaye ba.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da korafe korafe kan Buhari game da taimaka masa a 2015

Ya kuma zargi Baba-Ahmed da kokarin amfani da sunayen Kwankwaso da Obi domin jawo hankalin jama’a.

“Tun da Peter Obi da madugu suka zama abin magana a kasar nan, kowa yana son ya ja hankalin mutane ta hanyar ambaton sunayensu,” in ji shi.
Hakeem Bsba.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Dr. Hakeem Baba Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Habeeb Mohammed ya jaddada cewa babu lokacin da Kwankwaso ko Obi suka je PRP domin neman tikitin shugaban kasa, kamar yadda Punch ta ruwaito shi yana fada.

A halin yanzu, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun shiga jam’iyyar NDC, inda ake ganin suna shirin cika burinsu na samun takara gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kwankwasiyya ta soki Malam Shekarau

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Kwankwsiyya ta ragargaji tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau kan zargin cewa Rabiu Musa Kwankwaso na yi wa Bola Tinubu aiki a boye.

An rawaito cewa Shekarau ya ce shi da Kwankwaso duk suna aiki domin Tinubu ya sake cin zaɓe, sai dai Kwankwaso yana yin hakan ne a ɓoye.

Kwankwasiyya ta bayyana kalaman da aka danganta wa Ibrahim Shekarau a matsayin marasa tushe da kuma yunƙurin neman suna a siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262