Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau Ya Janye daga Neman Takarar Dan Majalisar Wakilai

Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau Ya Janye daga Neman Takarar Dan Majalisar Wakilai

  • Mai neman samun takarar dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Mahmud Sadis Buba ya janye daga neman kujerar a jam'iyyar APC
  • Matashin wanda aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye daga takarar a mazabar Sabon Gari karkashin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Buba ya ce matakin ya biyo bayan kokarin sulhu daga shugabannin APC, bayan tuntuba da iyali, abokan siyasa da masu ruwa da tsaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sabon Gari, Kaduna - Hon. Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye daga takarar da ya shiga karkashin APC.

Matashin ya janye ne daga neman takarar kujerar dan majalisar wakilai ta tarayya ta Sabon Gari karkashin jam’iyyar APC.

Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takara a APC
Matashi mai neman takarar majalisar wakilai, Mahmud Sadis Buba. Hoto: Mahmud Sadis Buba.
Source: Facebook

Ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar 16 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan

An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

Musabbabin janye neman takarar Mahmud Sadis Buba

A cikin wasikar da ya aikewa shugaban APC na Kaduna, Mahmud Buba ya bayyana cewa daukar matakin janyewar ba abu ne mai sauki ba.

Ya ce kokarin sulhun da shugabannin jam’iyya suka fara ne ya sa ya gaggauta yanke shawarar.

Buba ya ce bayan tattaunawa mai zurfi da iyalansa, abokan siyasarsa da masu ruwa da tsaki a APC, ya fahimci cewa hadin kai bayan dan takara shi ne mafita, ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen samun nasara a babban zabe.

'Dan siyasar ya yaba wa gwamnan Kaduna, Uba Sani, da shugabannin APC saboda damar da suka ba shi wajen shiga tsarin tantance ‘yan takara, ya ce wannan dama ta kara masa gogewa a siyasa.

Mahmud Sadis Buba ya janye daga takara a APC
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Matsayar Mahmud Buba a jam'iyyar APC

Mahmud Buba ya ce har yanzu yana da cikakken biyayya ga APC, yana mai jaddada cewa janyewarsa ba alamar gazawa ba ce.

Kara karanta wannan

Bayan Pantami, malamin Musulunci, Sheikh Bashir ya rasa takarar gwamna a Sokoto

Ya bayyana hakan a matsayin sadaukarwa domin maslahar jam’iyyar da ci gaban mazabarsa.

Ya kuma tabbatar da cewa zai yi aiki tukuru domin ganin dan takarar da APC ta amince da shi ya samu nasara a zabe.

Buba ya ce zai ci gaba da mara wa jam’iyyar baya a dukkan matakai, ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankula tare da kasancewa cikin hadin kai.

Ya shawarce su da su goyi bayan duk wanda APC ta tsayar a matsayin dan takarar mazabar Sabon Gari.

A baya dai an yi ce-ce-ku-ce kan shekarun Buba yayin neman tikitin APC, wasu masu suka sun yi ikirarin cewa yana da shekaru 16, bayan yada bayanan da ke shafin fasfo dinsa.

Tambuwal ya janye daga takarar sanata

An ji cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nuna dattaku a jihar Sokoto yayin fitar da ƴan takara a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya.

Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a karkashin ADC domin bai wa tsohon kwamishina damar samun kujera.

Jam’iyyar ADC ta ce Tambuwal ya dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da karfafa dimokuradiyya cikin gida gabanin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.