Wata Sabuwa: Yadda Trump Ya Tsara 'Guduwa' daga Yakin da Ya ke da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump na nazarin yiwuwar kawo ƙarshen yaƙi da Iran tare da ayyana cewa Amurka ta samu nasara, ba tare da cimma wata sabuwar yarjejeniyar nukiliya da Tehran ba
- Wani Rahoton ya ce Trump ya tattauna wannan lamarin a sirrance da wasu manyan mashawartansa, yayin da ake ƙoƙarin ganin an tsawaita tsagaita wutar da ake yi tsakanin ƙasashen biyu
- Rahoton ya ƙara da cewa Trump na ganin matakan da Amurka ta ɗauka sun raunana shirin nukiliyar Iran, kuma barazanar sake kai hare-hare na iya zama hanyar hana Tehran sake gina makaman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka, Donald Trump na nazarin yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin da Iran tare da ayyana nasara ba tare da cimma yarjejeniyar nukiliya da Tehran ba, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.
Hakan na zuwa ne bayan shafe watanni ana fafarawa tsakanin kasashen ba tare da cimma yarjejeniya kan nukiliya da sauran abubuwa ba.

Source: Getty Images
Wall Street Journal ta ruwaito cewa wasu jami'an Amurka sun ce Trump ya yi magana da manyan mashawartansa a sirrance.
Shirin Trump kan kasar Iran
A cewar jami'an, Trump zai fi samun damar tsawaita tsagaita wutar “har abada” idan aka tabbatar da cewa Iran ba ta iya farfaɗo da shirinta na nukiliya kuma an dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar ruwan Hormuz.
Jami'an sun ce Trump ya bayyana wa manyan mashawartansa cewa Tehran na iya kasancewa ba ta da damar sake farfaɗo da ayyukan nukiliyarta bayan barnar da aka yi wa muhimman cibiyoyin nukiliyar ƙasar.
Rahoton Jerussalem Post ya ce harin da aka kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yunin 2025 ya yi wa kayayyakin more rayuwar shirin nukiliyar ƙasar mummunar illa.
Trump ya dogara da leƙen asiri
A cewar rahoton, Trump na ganin cewa bayanan leƙen asirin Amurka za su iya gano duk wani yunƙurin Iran na sake gina cibiyoyin nukiliya ko kuma ƙoƙarin ƙera makamin nukiliya a ɓoye.
Rahoton ya ce Trump ya bayyana a wasu tarurrukan baya-bayan nan cewa yiwuwar Amurka ta sake kai hari ga Iran idan ta yi yunƙurin farfaɗo da shirinta na nukiliya.

Source: Getty Images
Jami'an sun kuma yi hasashen cewa Trump zai ɗage takunkumin da sojojin ruwan Amurka suka sanya kan tashoshin jiragen ruwa na Iran idan Tehran ta sake buɗe mashigar ruwan Hormuz gaba ɗaya.
An kori manyan jami'an Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Hukumar Leken Asirin Isra'ila ta Mossad, Roman Gofman, ya cire wasu manyan jami'ai biyu da ake zargin suna da hannu wajen tsara wani shirin kifar da gwamnatin Iran da bai yi nasara ba.
Gidan talabijin na Isra'ila ya ruwaito cewa ɗaya daga cikin jami'an shi ne shugaban sashen leƙen asiri na Mossad tun watan Disamba, yayin da ɗayan kuma shi ne shugaban sashen da ke kula da harkokin Iran.
Rahoton ya ce jami'an biyu na cikin waɗanda suka tsara wani shirin rubutacce na kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar amfani da ƙananan ƙabilu da kuma ƙarfafa zanga-zanga.
Asali: Legit.ng

