An Sanya Sunayen 'Yan Takarar Gwamna na ADC Su 28 a Shafin INEC

An Sanya Sunayen 'Yan Takarar Gwamna na ADC Su 28 a Shafin INEC

  • Babbar jam’iyyar ADC ta saka bayanan ‘yan takararta 28 na kujerar gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a shafin INEC
  • Kakakin jam’iyyar ya ce ADC ta cika wa’adin da aka tsawaita domin gabatar da sunayen ‘yan takararta na gwamna a zaɓen 2027
  • Sai dai sunan ɗan takarar gwamna na Enugu ne kawai bai shiga ba saboda rikicin shugabanci da ya taso bayan zaɓen fidda gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam’iyyar ADC ta saka bayanan ‘yan takararta 28 na gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi a shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Jam’iyyar ta kammala aikin ne a cikin wa’adin da INEC ta tsawaita domin shigar da bayanan ‘yan takara na zaɓen 2027.

Shugaban jam'iyyar ADC na kasa
Tambarin ADC a gefen hagu da shugaban jam'iyyar a dama. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

Enugu ce kawai ba a saka ba

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Mai neman takarar gwamnan PDP a Gombe ya fice daga jam'iyyar

The Nation ta wallafa cewa sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce sunan ɗan takarar gwamna na jihar Enugu ne kawai bai shiga cikin bayanan ba.

Bolaji Abdullahi ya ce har yanzu ana fama da rikicin shugabanci da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a jihar.

Abdullahi ya ce kammala shigar da bayanan ya biyo bayan tura sunayen ɗan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya da jam’iyyar ta yi a baya.

Ya ce hakan ya sanya ADC ta cika sabbin buƙatun INEC na gabatar da sunayen ‘yan takara.

INEC ta tsawaita wa’adin

INEC ta fara sanya ranar 8 ga Agusta a matsayin ranar ƙarshe da jam’iyyun siyasa za su saka bayanan ‘yan takararsu na gwamna da Majalisar Dokokin Jihohi.

Sai dai daga bisani hukumar ta ƙara wa’adin da kwanaki uku, inda ta mayar da ranar ƙarshe zuwa 11 ga Agusta.

Ƙarin wa’adin ya biyo bayan ƙoƙarin da jam’iyyu da dama ke yi na kammala shigar da bayanan ‘yan takararsu sakamakon wasu matsalolin fasaha da na gudanar da aiki.

‘Yan takarar ADC sun yi rantsuwa

Kara karanta wannan

ADC: 'Abu 1 da zai hana jam'iyyar su Atiku nasara a zaɓen Osun'

Wannan na zuwa ne yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, suka yi rantsuwar cewa ba za su yi amfani da dukiyar jama’a ba ta hanyar da ba ta dace ba.

Abdullahi ya ce duk wanda aka zaɓa a ƙarƙashin ADC zai sanya hannu kan yarjejeniyar tare da yin rantsuwar da za ta sanya shi abin tambaya idan ya karya ƙa’idojin.

The Cable ta rahoto cewa rantsuwar ta ƙunshi gaskiya, riƙon amana, yin aiki bisa ka’ida da kuma amfani da dukiyar jama’a bisa doka.

Atiku abubakar VP da Rotimi Amaechi
Dan takarar shugaban kasa na ADC da mataimakinsa. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Haka kuma, dokar ta tanadi cewa duk wani jami’in da aka zaɓa ko aka naɗa da ya yi murabus daga ADC ko ya sauya sheka, zai rasa kujerar da ya samu ƙarƙashin jam’iyyar.

Atiku ya nemi Osun ta zaɓi ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya nemi al’ummar Osun su zaɓi jam’iyyar a zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta.

Atiku ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ta ƙunshi mafi kyawun ‘yan Najeriya yayin babban taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Osogbo.

Ya kuma tuna da irin goyon bayan da al’ummar Osun suka ba shi a baya, ciki har da lokacin da ya je jihar domin yaƙin neman zaɓen Ademola Adeleke da kuma lokacin da ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng