Majalisar Tarayya Ta Tsaida Lokacin Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

Majalisar Tarayya Ta Tsaida Lokacin Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

  • Majalisar tarayya ta kafa wani kwamiti da zai yi bitar kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kamar yadda aka sabunta
  • Ko a baya, akalla sau shida majalisar ta yi kokarin bitar kundin don sabunta wasu dokoki amma hakan ba ta yiwu ba
  • Mataimakin kakakin majalisar, Mista Benjamin Kalu ya ce wannan sabon kwamitin zai kammala bitar zuwa karshen shekarar 2025

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar tarayya ta tsayar da watan Disamba na shekarar 2025 a matsayin wa'adin kammala aikin bitar kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki, kuma mataimakin kakakin majalisar wakilai, Mista Benjamin Kalu ya bayyana haka a taron share fage na bitar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban banki CBN kan muhimman batu 2

Majalisar tarayya ta fara gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, an samu karin bayani
Majalisar tarayya ta fara gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, an samu karin bayani. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Za a saka sabbin dokoki a kundin mulkin kasar

Leadership ta ruwaito Mista Kalu ya na cewa, akwai bukatar yin bitar kundin tsarin mulkin na 1999 da aka tsara wa gwamnatin farar hula a shekarar 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shugaban kwamitin, majalisar a halin yanzu tana aiki kan wasu kudirori 40 da ke kan matakai daban-daban da suka shafi sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Ba ayi nasarar sabunta kudin mulkin kasar ba a baya

Mataimakin shugaban majalisar ya ce kwamitin zai yi aiki tare da kwararru, masu ba da shawara da lauyoyi wajen sake fasalin kundin mulkin kasar.

Mista Kalu ya yi nuni da cewa sau shida majalisar na yunkurin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar ba tare da wata nasara ba, rahoton Radio Nigeria.

Ya yi kira ga mambobin kwamitin da su fito da kudirorin da za su wakilci muradun kasa tare da yin aiki kafada da kafada da kwamitin majalisar dattawa kan kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Sun fi na Buhari, Shehu Sani ya fadi abin da ya kamata a yi wa hafsoshin tsaro, ya shawarci mutane

Gyara kudin tsarin mulkin Najeriya bata lokaci ne - NEF

A wani labarin makamancin wannan, kungiyar manyan Arewa ta NEF, ta ce bata lokaci ne da asarar dukiyar al'umma yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima.

Daraktan yaɗa labaran kungiyar na wancan lokaci, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Rahotanni a lokacin sun nuna cewa majalisar tarayya ta ware naira biliyan 1 don gyara fasalin kudin tsarin mulkin ƙasar, wanda Baba-Ahmed ya nemi 'yan Najeriya su yi adawa da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel