Amurka Ta Fara Fuskantar Matsalar Makamai, Trump Ya Dakatar da Hare Hare kan Iran
- Rahotanni daga Amurka sun tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump ya dakatar da kai hare-hare a Iran
- An tabbatar da cewa Shugaba Trump ya ɗauki matakin ne game da kan Iran bayan kwanaki 13 na farmaki a jere
- An ce Trump ya yanke shawarar ne bayan ganawa da manyan masu ba shi shawara, saboda fargabar raguwar makaman kariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - hotanni sun tabbatar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da shirin kai sababbin hare-hare a Iran.
Wannan mataki ya biyo bayan kai hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan kwanaki 13 ana kai farmaki.

Source: Facebook
The New York Times, tana ambaton jami'an gwamnatin Trump, ta ce shugaban ya yanke wannan shawara ne saboda fargabar cewa ci gaba da yakin zai rage makaman kariya na Patriot.
Gargadin Trump ga Iran da wasu ƙasashe
Wannan na zuwa kwana kadan bayan Trump ya yi barazana ga Iran, China da wasu ƙasashe masu yawa a duniya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya ƙasashe 23 cikin matakin gargadi mafi girma na "kada a yi tafiya" zuwa cikinsu.
Ƙasashe 11 daga nahiyar Afirka na cikin jerin, yayin da Najeriya ta ci gaba da kasancewa a mataki na uku har yanzu.
Duk da cewa gargadin bai shafi Najeriya kai tsaye ba, Amurka ta ware wasu jihohin Najeriya da ta ce suna cikin hadari sosai.
Musabbabin ɗaukar mataki da Trump ya yi
Rahoton ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawa da Trump, manyan masu ba shi shawara da manyan jami'an majalisar ministocinsa a ranar Juma'a.
Har ila yau, wasu majiyoyi sun ambato cewa har yanzu ba a tabbatar ko dakatarwar ta wucin gadi ce ko kuma za ta ci gaba.
Rahoton ya kara da cewa matakin Trump ya nuna yana son ba diflomasiyya karin dama tare da fahimtar cewa hare-haren da ake kaiwa yanzu sun kai iyakar tasirinsu.
Sai dai majiyoyin sun ce sojojin Amurka na ci gaba da shirya tsare-tsaren yiwuwar komawa manyan hare-haren soja idan yanayi ya sauya.
Ƙarin bayani na tafe ....
Amurka za ta janye tallafi ga Najeriya
Mun ba ku labarin cewa Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da duk tallafin Amurka ga ƴan Najeriya da kasar baki daya.
Masana sun gargadi cewa idan kudirin ya zama doka, shirye-shiryen HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, rigakafi da lafiyar mata da yara za su shiga hadari.
Sun bukaci gwamnatin Najeriya ta inganta tsaro, karfafa dangantaka da Amurka, tare da samar da hanyoyin cikin gida domin daukar nauyin lafiya.
Asali: Legit.ng

