2027: Yusuf Buhari Ya Fara Hada kan Jama'a, Ya Nada Hadimi na Musamman
- Dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya fara shiga jama'a domin tallata manufofinsa game da takarar da zai yi a zaben 2027
- A wani mataki na hada kan jama'a, Yusuf Buhari ya nada Aliyu Haruna Daura a matsayin wanda zai jagoranci hulda da jama'a a kamfen din shi
- 'Yan Najeriya da dama sun yi martani kan sanarwar da Yusuf Buhari ya fitar, wasu na yaba masa wasu kuma na cewa har yanzu akwai aiki a gabansa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Yayin da 'yan siyasa ke cigaba da shirye-shiryen fuskantar zaben 2027, dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya fara hada kan jama'a.
Yusuf Buhari ya fara nada mutanen da za su jagoranci yakin neman zaben da zai yi domin samun zama dan majalisar wakilai a 2027.

Source: Facebook
Yusuf Buhari yana hada kan jama'a
Legit ta tattaro bayanan da Yusuf Buhari ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 6 ga watan Mayun 2026.
Dan tsohon shugaban kasar ya wallafa cewa:
"A yayin ziyarata ta baya-bayan nan a mazabarmu, mun yi mu’amala sosai da al’ummarmu, mun saurari damuwarsu da abubuwan da suke fata.
"Hakan ya kara karfafa kudurinmu yayin da muka fara hada kan jama'a domin tabbatar da samun nasara tare."
Wane ne wanda Yusuf Buhari ya ba mukami?
Yusuf Muhammadu Buhari ya nada Alhaji Aliyu Haruna Daura shugaban hulda da jama'a da hada kan mutane domin takarar da zai yi a zaben 2027.
Sanarwar da ya fitar ta ce:
"Ina farin cikin sanar da kai an nada ka a matsayin shugaban hulda da jama’a da hada kan mutane a cikin tsarin yakin neman zabena na kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Daura, Sandamu da Mai’adua a zaben 2027 mai zuwa."
"Wannan mukami yana da muhimmanci wajen tabbatar da isar da sakonni da kuma hada kan jama’a. Wannan nadin ya nuna amincewarmu da kwarewarka da kuma jajircewarka".

Source: Facebook
Martanin 'yan Najeriya
'Yan Najeriya da dama sun yi martani a kafar X bayan sanarwar da Yusuf Muhammadu Buhari ya fitar, inda wani 'dan siyasa a Kaduna, Hon. Nuhu Sada ya ce:
"Ziyara da tuntuba na da muhimmanci, amma ainihin shugabanci shi ne aiki. Jama’a ba za su damu da kalamai kawai ba, suna so su gani a kasa."
Malam Mali Flash ya ce:
"Allah Ya datar da kai a wannan tafiya mai albarka."
Sambo ya bayyana cewa:
"Muna fatan wadannan damuwowi da aka ce ka saurara ba za su tsaya a matsayin bayanan kamfe kawai ba. Jama’a suna bukatar canji na gaskiya, ba alkawari kawai ba, Yusuf."
Abdul Gama ya ce:
"Muna fatan za ka yi koyi da Buhari wajen rike amana da gaskiya, tare da fifita jin dadin jama’a."
Yusuf Buhari ya gana da Dikkp Radda
A wani labarin, kun ji cewa dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya gana da gwamna Dikko Umaru Radda a Katsina.
Gwamna Radda ya gana da Yusuf ne bayan sayen fom din neman takarar majalisar wakilai domin wakiltar mazabar Daura, Sandamu da Mai’adua.
Yusuf Buhari ya bayyana cewa zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya yi riko da gaskiya da amana idan aka amince aka zabe shi a zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


