Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Ci Tarar Wanda Ya Nemi a Rushe Babban Taron APC na Kasa

Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Ci Tarar Wanda Ya Nemi a Rushe Babban Taron APC na Kasa

  • Kotu ta yi fatali da karar da aka nemi ta soke babban taron APC na kasa, ta ce ba ta hurumin tsoma baki a harkokin jam'iyyu na cikin gida
  • Fubara Dagogo, wanda ya ayyana kansa a matsayin mamban APC ne ya shigar da karar, inda ya zargi APC da hana shi neman kujerar shugabanci
  • Kotun ta kuma ci tarar mai kara da lauyansa jimullar kudi Naira miliyan 20 domin biyan wadanda ake kara a shari'ar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar kotun tarayya, Abuja ta yi watsi da karar da wani mamban APC, Fubara Dagogo ya shigar, inda ya nemi a soke babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar kwanan nan.

A hukuncin da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke ranar Litinin, kotun ta ce ba ta da hurumin sauraron karar saboda batutuwan da aka gabatar suna da alaka da harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Shugaban APC na kasa.
Shugaban jam'iyyar SPC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a taron tara shi murna a hedkwatar jam'iyya da ke Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

The Nation ta ce alkalin ta bayyana cewa batutuwan da suka shafi tantance ‘yan takara da sayen fom na takara al’amura ne da suka shafi jam’iyya kawai, wanda kotu ba ta da ikon tsoma baki a ciki.

Kotu ta ci tarar mai kara da lauyansa

Kotun ta amince da bukatar farko da wadanda ake kara suka gabatar, sannan ta yi watsi da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/591/2026 da aka shigar tun ranar 23 ga Maris, 2026.

Mai Shari’a Abdulmalik ta dogara da sashe na 83(6) na dokar zabe ta 2026 wajen sanya tarar Naira miliyan 10 ga mai karar da kuma lauyansa, Chief Sir O.A.U. Onyema.

Hakan na nufin an ci su tarar Naira miliyan 20 baki daya domin biyan wadanda ake kara hudu a shari’ar.

Wadanda aka gurfanar sun hada da APC, shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, mataimakin shugaban APC na kasa (Kudu maso Kudu), Victor Giadom, da sakataren tsare-tsare, Sulaiman Muitamma.

Kara karanta wannan

Dan damfara ya sace wa mahajjaciya 'yar Najeriya daloli a Madina

Korafin da Dagogo ya gabatar a kotu

Dagogo ya yi zargin cewa an hana shi damar sayen fom din nuna sha’awa da na takara domin neman kujerar mataimakin shugaban APC na kasa daga yankin Kudu maso Kudu, in ji Daily Post.

Daga cikin bukatun da ya gabatar a kotu akwai neman a soke duk wani taro ko zaben da aka gudanar kan kujerar mataimakin shugaban APC na yankin Kudu maso Kudu ba tare da sanya shi a ciki ba.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a harkokin zaman shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya roki kotun ta bayyana cewa saboda rasidin biyan kudin fom mai lamba 26827 da aka ba shi ranar 13 ga Maris, yana da hakkin samun fom din nuna sha’awa da na takara domin neman kujerar.

Dagogo ya kuma nemi kotun ta tilasta wa wadanda ake kara na uku da na hudu su biya shi diyyar Naira miliyan 100 saboda kunyata shi da kuma azabar da ya ce ya sha sakamakon lamarin.

APC ta tantance gwamnoni 12

A baya, an ji cewa jam’iyyar APC ta fara tantance gwamnoni masu neman wa’adi na biyu da masu neman takarar Sanata gabanin zaɓukan fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Jonathan ya kalubalanci wanda ya nemi hana shi fitowa takarar shugaban kasa a 2027

An ruwaito cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnoni a ranar 20 ga watan Mayu, yayin da na sanatoci zai gudana a ranar 18 ga watan Mayu, 2026.

APC ta tantance gwamnoni 12 ciki har da na Kano, Abba Kabir Yusuf kuma ta sahale masu su nemi tazarce a kan mulki a babban zaben 2027,

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262