Jonathan Ya Amsa Kiran 'Yan Najeriya, Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a Jam'iyyar PDP
- Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP
- Rahoto na musamman ya nuna cewa kungiyoyi daban-daban daga ciki da wajen Najeriya suna fafatawar saya wa Jonathan fom din takara
- Masu goyon bayansa sun bayyana cewa burinsa shi ne ya sake dawo da martabar tattalin arzikin kasa da rage radadin talauci da ya addabi Najeriya
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya shirya tsaf domin neman komawa gidan gwamnati ta hanyar amfani da PDP a matsayin jam’iyyar cimma burinsa na siyasa a zaben 2027.
Wani babban jami'i a tawagar Jonathan ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi, ya ce an dauki wannan matakin ne bayan doguwar tattaunawa kan inda tsohon shugaban kasar ke da mafi girman damar samun nasara.

Kara karanta wannan
Masu neman takara 6 sun hakura, an bar wa Shekarau tikitin sanatan Kano ta Tsakiya

Source: Twitter
2027: Goodluck Jonatha zai tsaya takara a PDP
Jaridar Vanguard ce tilo ta fitar da wannan rahoto na musamman, inda ta ce jami'in ya shaida mata cewa:
"An yanke shawarar yin amfani da PDP ne bayan nazari kan inda damarsa ta fi bayyana wajen samar da shugabanci na kwarai ga kasar nan, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsananin rayuwa da talauci."
Jaridar ta ce a yanzu haka, akwai gasa da ake yi tsakanin kungiyoyi daban-daban wadanda ke son nuna soyayyarsu ta hanyar sayen fom din takara na N100m ga Jonathan.
Tun da cewa wa'adin saye da mika fom din zai kare a ranar Talata mai zuwa, kungiyoyin suna fafutukar ganin sun riga juna mallakar fom din ga tsohon shugaban kasar.
Kungiyoyin da ke son saya wa Jonathan fom
Daga cikin kungiyoyin da ke sahun gaba akwai Goodluckan Movement wadda ta kunshi yan Najeriya mazauna kasashen waje, wadanda ke jayayyar cewa su ne suka fi dacewa su sayi fom din.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban kasa, Jonathan ya canza jam'iyya don ya fito takara a 2027? Gaskiya ta bayyana
Sauran sun hada da Coalition for Jonathan, The New Nigeria (TNN) wadda ke da mambobi miliyan biyu a arewacin Najeriya, da kuma wasu kungiyoyin matasan arewa kamar Almajiri Network da Arewa for Good Governance.
Shirin ceto tattalin arziki
Duk da cewa a baya Jonathan ya shaida wa dandazon matasan da suka nemi ya tsaya takara cewa zai yi shawara tukuna, rahoton jaridar ya nuna cewa tuni ya kammala yanke shawararsa.

Source: Twitter
Babban burinsa a cewar rahoton shi ne ya lallashi yan Najeriya su sake ba shi dama domin ya farfado da tattalin arzikin kasa wanda ke cikin wani mawuyacin hali a yanzu.
Gwamnatin Jonathan ta taba fuskantar kalubale a baya, amma masu goyon bayansa suna ganin cewa kwarewarsa da kuma salon shugabancinsa na zaman lafiya sune abubuwan da Najeriya ke bukata a yanzu domin fita daga kangin da ake ciki.
Yanzu dai an zura idanuwa a ga lokacin da Jonathan zai cika fom ya mika wa PDP gabanin cikar wa'adi a ranar Talata, da kuma yadda shigar Jonathan takarar zai iya sauya siyasar 2027.
2027: Jonathan ya sauya jam'iyya?
A wani labari, mun ruwaito cewa, PDP tsagin Tanimu Turaki ta musanta fastocin Goodluck Jonathan da ake yadawa,da ke nuna ya fice daga jam'iyyar zuwa wasu.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar na nan a cikinta, kuma ya sabunta rijista a mazabarsa da ke jihar Bayelsa kwanan nan.
Bangaren Turaki ya ce dole ne a yi wannan bayani saboda tanadin dokar zabe da ta haramta mutum ya yi rajista a jam’iyya fiye da daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
