Gwamna Ya Fara Samun Matsala kan Ɗan Takara, Tsohon Shafeta Janar Zai Kara da Zabinsa

Gwamna Ya Fara Samun Matsala kan Ɗan Takara, Tsohon Shafeta Janar Zai Kara da Zabinsa

  • Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda ya shiga takarar gwamnan Yobe bayan yarjejeniyar tsayar da ɗan takara guda ta rushe
  • Dattijon ya bayyana cewa wasu ‘yan takara huɗu sun karɓi fom ɗin tsayawa takara, lamarin da ya nuna shirin sasanci tsakanin masu neman kujera ya gaza
  • Tsohon shugaban ‘yan sandan ya ce zai iya janyewa daga takara idan shugabannin jam’iyya suka gabatar masa da sharuddan da ya amince da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya shiga takarar gwamnan Yobe.

Majiyoyi sun ce tsohon ɗan sandan ya shiga tafiyar ce bayan shirin samar da ɗan takarar sasanci tsakanin masu neman kujera ya rushe.

Tsohon ɗan sanda ya sayi fom din takara a Yobe
Tsohon sufeta-janar na ƴan sanda, Usman Alkali Baba da Gwamna Mai Mala Buni. Alkali Usman Baba Support Group, Mamman Mohammed.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Lahadi 3 ga watan Mayun 2026 a Damaturu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tayar da rigima kan hana shi takarar gwamna, ya soki APC

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Mai Mala Buni ya tsayar da wanda ya ke so ya gaje shi a matsayin gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Tsohon shugaban yan sanda zai yi takara

Alkali ya ce wasu ‘yan takara huɗu sun riga sun karɓi fom ɗin tsayawa takara, abin da ya tabbatar masa cewa yarjejeniyar sasanci tsakanin masu neman kujerar ta lalace gaba ɗaya.

Ya ce:

“Saboda haka na karɓi fom domin shiga takarar. Babu wanda ya nuna min inda zan sanya hannu ko kuma ya nemi na yi magana.”

Tsohon shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa fahimtarsa game da tsarin sasanci na jam’iyya ita ce masu neman takara su amince su mara wa mutum guda baya domin haɗin kai.

Yobe ta dauki zafi game da takarar gwamna
Taswirar jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Dalilin Alkali na ci gaba da neman takara

Alkali ya ce yanzu da hakan bai tabbata a Yobe ba, ya yanke shawarar ci gaba da neman kujerar gwamna domin cika burinsa na siyasa a jihar.

Ya ƙara da cewa ya isa Damaturu ne domin tabbatar da ingancin fom ɗinsa tare da tuntubar dokokin jam’iyya da kuma masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar matakin.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya musanta fitowa takarar shugaban kasa a inuwar ADC

Da aka tambaye shi ko zai iya janyewa idan shugabannin jam’iyya suka buƙaci ya goyi bayan wani ɗan takara, Alkali ya ce hakan zai danganta da sharuddan da za a gabatar masa.

Ya ce:

"Zan iya amincewa idan na gamsu da sharuddan.”

Sannan ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da nuna biyayya da jajircewa yayin gudanar da zaɓen fitar da gwani domin fitar da dan takara da ya dace da al'ummar Yobe.

Sanata Bomai ya sayi tikitin takara

Mun ba ku labarin cewa an fara samun matsala a siyasar jihar Yobe bayan sanata daga jihar ya yi watsi da ɗan takarar gwamna da wasu shugabannin APC suka goyi baya.

Sanata Ibrahin Mohammed Bomai ya ce zaɓen Baba Malam Wali da aka yi ba matsayar dukkan masu ruwa da tsaki ba ce, illa ra’ayin mutum guda.

Dan majalisar Kudancin Yobe ya bayyana cewa duk wani yunƙurin kakaba ɗan takara ya saɓa wa dimokuraɗiyya, yana mai alƙawarin kare haƙƙin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.