Zulumi da Kunci Sun Lullube Sojojin Amurka da Suka Yi Kwana 250 a Teku

Zulumi da Kunci Sun Lullube Sojojin Amurka da Suka Yi Kwana 250 a Teku

  • Rahotanni sun ce dubban sojojin Amurka da ke cikin jirgin ruwan yaƙi na USS Abraham Lincoln na fuskantar ƙarancin abinci da matsalolin ruwa
  • Wasu sojojin sun kuma bayyana gajiya da matsalolin lafiyar kwakwalwa bayan shafe sama da kwanaki 250 a teku ba tare da komawa gida ba
  • ‘Yan majalisar dokokin Amurka sun nemi Pentagon ta yi bayani kan yanayin sojojin da kuma tsawon lokacin da ake tura jiragen ruwan yaƙi cikin teku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Yanayin rayuwar dubban sojojin Amurka da ke cikin jirgin ruwan yaƙi na USS Abraham Lincoln ya jawo damuwa bayan jirgin ya shafe sama da kwanaki 250 a teku.

Rahotanni sun ce sojojin na fuskantar ƙarancin wasu kayan yau da kullum, matsalolin ruwa da kuma gajiya sakamakon tsawaita zaman su a teku.

Kara karanta wannan

Amurka ta nuna ba daga kafa, ta caccaki Isra'ila kan taba kawayen Iran a Lebanon

Jirgin Amurka na USS Abraham Lincoln
Babban jirgin Amurka na tafiya a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

‘Yan majalisa sun nemi bayani

BBC ta wallafa cewa Sanata Richard Blumenthal na jihar Connecticut ya bayyana wasu matsalolin da ake zargin sojojin ke fuskanta a cikin wata wasiƙa zuwa ga Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

Ya ce rahotannin sun haɗa da ƙarancin kayan amfani, matsalar gurɓacewar ruwa, matsalolin bututun ruwa da tabarbarewar lafiyar kwakwalwar sojoji.

Blumenthal ya kuma ambaci matsalolin tsaro na jirgin da kuma matsalar isar da wasiƙu da kayayyakin da iyalan sojoji ke turawa.

Ya ce matsalolin na buƙatar kulawa cikin gaggawa, tare da tambayar ko Rundunar Sojin Ruwan Amurka za ta iya ci gaba da irin wannan yanayin tura jiragen yaƙi.

An nemi a gudanar da bincike

Sanata Ruben Gallego ya nemi sojojin Amurka su bai wa tawagar ‘yan majalisa damar shiga jirgin domin gudanar da bincike.

The Guardian ta wallafa cewa Gallego ya ce babu wani dalili da zai hana ‘yan majalisar samun damar duba halin da sojojin ke ciki.

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun rasa rayukansu bayan faɗuwar jirgin saman yaƙi

Rahotannin kafofin watsa labaran soji sun kuma ce wasu iyalan sojojin sun nuna damuwa kan lafiyar kwakwalwar ‘yan uwansu da ke cikin jirgin.

Matsalar da sojoji ke fuskanta

Rahotanni sun ce wasu sojojin ba sa samun damar wanke tufafinsu na tsawon sama da mako guda.

Haka kuma, ana zargin cewa rashin yawan tsayawa a tashoshin jiragen ruwa na hana sojojin samun sababbin kayan abinci akai-akai.

Wani ɗan uwan soja ya ce danginsa da ke cikin jirgin ya rasa nauyin kilo 29 tun bayan fara wannan tafiya.

Ya ce sojan ya tabbatar masa cewa wasu sojoji sun taɓa ƙoƙarin tsalle daga jirgin.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump tare da sojojin Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma bayyana cewa sojan ya shaida masa cewa ya gaji sosai, yayin da hayaniya da girgizar injin jirgin da jiragen sama ke tashi da sauka ke ƙara masa wahala.

An tsawaita zaman jirgin a teku

USS Abraham Lincoln ya bar California a watan Nuwamba 2025 zuwa tekun Kudancin China kafin a tura shi Gabas ta Tsakiya gabanin hare-haren da aka kai wa Iran a watan Fabrairu.

Da farko an shirya kawo ƙarshen aikin jirgin a watan Mayun 2026, amma an ci gaba da tsawaita zaman sa a teku ba tare da bayyana ranar dawowarsa ba.

Kara karanta wannan

Duka bayanan da suka fito daga juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Tinubu

Rahotanni sun ce Amurka na shirin maye gurbin jirgin da USS George Washington a wani tsarin sauya jiragen da aka shirya tun da farko.

Leavitt za ta bar White House

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'ar yaɗa labarai ta Fadar White House, Karoline Leavitt, za ta bar mukaminta a ƙarshen watan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Leavitt a matsayin ɗaya daga cikin amintattun hadimansa, yana mai cewa za ta bar aikin ne domin ba da lokaci ga ƙananan ‘ya’yanta da iyalinta.

Trump ya ce Leavitt za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara daga wajen gwamnati da kuma murya mai tasiri a cikin Jam’iyyar Republican.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng