Zargin Ta'addanci: Kamfanoni da Mutane 9 da SEC Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
- Hukumar SEC ta umarci masu gudanar da harkokin kasuwar hannayen jari su daskarar da kuɗaɗe da kadarorin wasu mutane shida da kamfanoni uku
- An sanya sunayen mutanen da kamfanonin a jerin takunkumin Najeriya bisa zargin hannu wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar nan
- SEC da ke sanya ido a kan harkokin hannun jari ta ce duk wanda ya karya umarnin zai iya fuskantar tara, dakatar da aiki ko kuma soke rajistarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja - Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (SEC) ta umarci duk masu gudanar da harkokin kasuwar jari da su gaggauta daskarar da kuɗi, kadarori da sauran dukiyoyin wasu bayin Allah.
Wadannan mutane da aka kakabawa wannan takunkumi, ana zargin cewa su na da alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addancin da ya addabi Najeriya.

Source: Getty Images
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa umarnin na cikin wata sanarwa da hukumar ta aika wa dukkanin kamfanonin da ke ƙarƙashin kulawarta, bayan Kwamitin Takunkumin Najeriya (NSC) ya sanya sunayen mutanen da ƙungiyoyin cikin jerin takunkumin ƙasar.
SEC ta dauki mataki kan zargin ta'addanci
Leadership ta wallafa cewa an ɗauki matakin ne bisa tanadin Dokar Hana Ta’addanci da Haramta Ayyukan Ta’addanci ta shekarar 2022 domin dakile ayyukan yan ta'adda da ta'addanci a kasar nan.
Mutanen shida da aka ambata su ne Babangida Muhammed Adamu Hammajam, Abdullahi Umar Usman, Ibrahim Abubakar, Adamu Chiroma, Muktar Muhammad Adamu da Yakubu Ogirima Ibrahim.
Kamfanonin da aka ambata kuma su ne Nine to Nine BDC Ltd, Generation Currency BDC Ltd da Abbal Bako & Sons Bureau de Change (BDC).
Dalilin SEC na hukunta wasu yan Najeriya
A cewar SEC, an sanya sunayen mutanen ne bisa zargin cewa suna da hannu wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci, samar da tallafin kuɗi ko wasu abubuwa ga ƙungiyoyin ta’addanci.
Haka kuma ana zargin cewa su na sauƙaƙa hada-hadar kuɗaɗen da ke da alaƙa da ISWAP, ciki har da rassan ƙungiyar na Okene da Kogi.

Source: Getty Images
Haka kuma, an zargi kamfanonin canjin kuɗin guda uku da taimakawa wajen gudanar da harkokin kuɗaɗen da ke da alaƙa da hanyar samar da kuɗi ga ISWAP a Okene.
Wannan sabon umarni ya zo ne bayan wani matakin takunkumi da hukumar ta ɗauka a baya, inda ta umarci a daskarar da kadarorin wasu mutane 10 da kamfanoni uku da ake zargi da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a kasuwar hada-hadar kuɗaɗe ta Najeriya.
Asali: Legit.ng

