El Rufa'i Ya Samu Sassauci da Kotu Ta ba Shi Damar Jinya a Hannun ICPC
- Kotu a Kaduna ta bai wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, damar samun kulawar lafiya yayin da yake tsare a hannun ICPC
- Lauyoyin El-Rufai sun roƙi kotu da ta ba shi damar duba haƙora da idanunsa a wasu asibitocin Abuja duk da ICPC ta garƙame shi
- Hukumar ICPC ta ce za ta bi umarnin kotu tare da tabbatar da tsauraran matakan tsaro yayin da za ta saki tsohon gwamnan ya je asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna: Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana cewa babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta amince tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu damar zuwa jinya yayin da yake tsare.
Wannan hukunci ya biyo bayan roƙon jin ƙai da lauyoyin kare El-Rufai suka gabatar a gaban kotu yayin ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin almundahana da halatta kudin haram.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa El-Rufai da wani wanda ake tuhuma tare da shi mai suna Joel Adoga suna fuskantar tuhume-tuhume guda 10 a gaban Mai Shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke Kaduna.
Zargin ICPC kan El-Rufa'i
Jaridar The Cable ta wallafa cewa ana zarginsu da mallaka da karkatar da kuɗin da ake zargin an samu ta hanyar cin hanci, tare da aikata laifin halasta kudin haram.
Hukumar ICPC ta ce wannan ya saɓa wa dokar hana halasta kudin haram ta shekarar 2022. Dukkannin mutanen biyu dai sun musanta zarge-zargen da ake yi musu a gaban kotu.
A wata sanarwa da kakakin ICPC, John Odey, ya fitar, ya ce zaman kotun na ranar Laraba 6 ga watan Mayu, 2026 ya fi mayar da hankali ne kan bukatar El-Rufai na sassauta wasu daga cikin sharudan belinsa.
Sanarwar ta ce yayin zaman, lauyoyin kare El-Rufai sun roƙi kotu da ta umarci ICPC ta ba shi damar zuwa samun kulawar lafiya musamman domin duba hakora da kuma idanunsa a wasu cibiyoyin lafiya da ke Abuja.

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
Lauyoyin sun bayyana cewa suna son a ba shi damar zuwa Mile Dental Clinic da kuma Skipper Eye-Q Hospital domin samun kulawar da ake buƙata.
Alkali ya sassauta wa El-Rufa'i
Da yake yanke hukunci kan bukatar, Mai Shari’a Aikawa ya amince da roƙon tare da umartar ICPC ta riƙa raka El-Rufai zuwa asibitocin ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Source: Facebook
Kotun ta kuma ce dole ne jami’an hukumar su dawo da shi wurin da ake tsare da shi nan take bayan an kammala jinyar.
John Odey ya ce ICPC za ta mutunta umarnin kotun tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da tsare El-Rufai bisa doka har sai ya cika dukkan sharudan belinsa.
El-Rufa'i ya kuma samun cikas
A baya, mun wallafa cewa hukumar ICPC ta shigar da takardar martani a gaban kotu tana adawa da sabon bukatar beli da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar.
Babbar Kotun Kaduna ta dage sauraron karar neman belin El-Rufai zuwa ranar 13 ga Mayu 2026 bayan ICPC ta nemi karin lokaci domin nazarin sababbin takardu.
Kotu ta taba kin bayar da beli ga Nasir El-Rufa'i bisa zargin cewa akwai yiwuwar zai iya tserewa, hana bincike gudana da kuma yiwuwar yin tasiri kan shaidu da hujjoji.
Asali: Legit.ng
