Ganduje, Shekarau Sun Raka Garo Shiga Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano
- Sabon mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo da ya sha rantsuwar fara aiki ya shiga ofis a ranar Laraba, 6 ga Mayun shekarar 2026
- Tsofaffin gwamnonin Kano da wasu manyan 'yan siyasar jihar ne suka taka wa Murtala Sule Garo baya zuwa ofishin mataimakin gwamna
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa addu'o'i da fatan alheri yayin da ya raka shi zuwa ofis a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sabon mataimakin gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo ya fara aiki a hukumance a ofishinsa da ke gidan gwamnatin jihar.
Garo ya kama aiki ne a ranar Laraba 6 ga Mayun 2026, inda tsofaffin gwamnoni Malam Ibrahim Shekarau da Dr Abdullahi Umar Ganduje suka raka shi ofis.

Source: Facebook
Garo ya wallafa a Facebook cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Abdullahi T. Gwarzo; 'yan Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi da Alhassan Ado Doguwa na cikin wadanda suka raka shi ofis.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Hon. Yusuf Ahmad Badau, Hon. Abdullahi Mu’azu Babangandu, Mariya Bunkure da sauransu.
Jawabin Mutala Sule Garo a ofis
Da yake jawabi a wajen taron, Murtala Sule Garo ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa amincewar da ya yi da shi.
Sabon mataimakin gwaman ya kuma gode wa shugabanni da dattawan APC, musamman wadanda suka raka shi zuwa ofishin.
Garo ya ce:
“Na ji dukkan shawarwari da nasihohin da ku ka bayar. Ina tabbatar muku da cewa da yardar Allah zan yi aiki da su kuma zan kasance mai biyayya tare da yi wa Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf aiki yadda ya kamata.”
Bayanin cigaban jihar Kano
Garo ya sake jaddada kudirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na aiwatar da ajandar saka Kano a gaba, wadda ta fi mayar da hankali kan jin dadin jama’a ta hanyar zuba jari a ilimi, samar da ruwa, lafiya, samar da ayyukan yi da noma.
Ya kara da cewa gwamnatin na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki domin matasan jihar su cimma burinsu.

Source: Facebook
Hudubar da Ganduje, Shekarau suka yi masa
Tun da farko, tsofaffin gwamnoni Malam Ibrahim Shekarau da Dr Abdullahi Umar Ganduje sun shawarci mataimakin gwamnan da ya kasance mai hakuri da biyayya, suna masu cewa irin wadannan dabi’u ne za su taimaka masa wajen samun nasara.
Ganduje ya wallafa a X cewa:
“A yau a Kano, na hada kai da sauran manyan shugabanni wajen shaida fara aiki a hukumance da sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Mai Girma Murtala Sule Garo.
“Ina taya shi murna tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi damar jagoranci cikin nasara wajen yi wa jihar Kano hidima.”
An kashe mutane bayan nada Murtala Garo
A wani labarin, mun kawo muku cewa ana cigaba da alhini kan mutane biyar da aka kashe a jihar Kano bayan rantsar da Mutala Garo.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan daba ne dauke da makamai masu hadari suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Kungiyar Amnesty International da ke rajin kare hakkin dan Adam ta yi Allah wadai da lamarin tare da kira ga gwamnati ta dauki mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


