'Ka Yi da Matata, In Yi da Matarka,' An Kama Abokai da Ke Musayar Matansu a Bauchi
- Rundunar Hisbah ta jihar Bauchi ta kama wasu abokai bisa zargin gudanar da wata dabi'a ta musayar matansu na aure a tsakaninsu
- Wadanda aka kaman sun bayyana cewa suna yin wannan ne na tsawon kwanaki a matsayin 'auren mutu'a' ba tare da wata ƙa'ida ta shari'a ba
- Daya daga cikin mazajen ya ce a cikin mafarki ne aka nuna masa dacewar ya rika bada aron matarsa, shi ma yana karbar aron matar wani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi - Rundunar Hisbah ta tabbatar da kama 'yan ƙungiyar "Wuddadu" a Azare, hedkatar ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi, bisa zargin yin musayar matansu na aure.
Wannan lamari ya tayar da hankulan jama'a tare da nuna fargaba kan yadda tarbiyya ke lalacewa a cikin al'umma.

Source: Facebook
An kama abokai da ke musayar matansu
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa mambobin wannan ƙungiya, wadanda abokai ne, suna ba juna aron matansu na tsawon wasu kwanaki, suna masu fakewa da sunan 'auren mutu'a'.
Kwamandan Hisbah na shiyyar Azare, Malam Ridwan Muhammad Khairan, ya tabbatar da cewa an kama waɗanda ake zargin ne bayan samun rahotanni daga mazauna garin da kuma wasu mambobin ƙungiyar da suka damu da lamarin.
Ya bayyana cewa rundunarsa ta musamman mai suna “Operation Ko Ba Kobo” ce ta kai samamen da ya yi sanadin cafke abokan da matansu a maɓoyarsu da ke cikin birnin.
Kwamandan ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa cewa su suka ƙirƙiri wannan tsarin aure da kansu ba tare da amincewar addini ko shari'a ba.
Dalilin wani matashi na bada aron matarsa
Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayyana cewa shigarsa wannan harka ta faru ne sakamakon wasu mafarkai da yake yawan yi, waɗanda yake ganin sun halatta masa yin hakan.
Sai dai mahukuntan Hisbah sun yi watsi da waɗannan iƙirari, suna masu bayyana su a matsayin marasa tushe da kuma tunanin da ke ɓatar da Musulmi.
Mazajen da ake zargin dai sun riga sun nuna damar wadannan 'munanan ayyuka' da suka aikata tare da yin alkawarin watsar da al'adar, yayin da Hisbah ke ci gaba da bincike, da yiwuwar shigar da su kara kotu.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar Wuddadu a Azare, Malam Sagir, ya bayyana cewa ƙungiyar ta kwashe shekaru biyu tana ƙoƙarin shawo kan halayen waɗannan mutane ta hanyar gargaɗi da shawarwari, amma abin ya faskara domin suna yin abun ne a sirrance.
Malam Sagir ya jaddada cewa:
“Shawarar kai rahoton lamarin ga rundunar Hisbah ta zama dole domin hana ci gaba da lalacewar tarbiyya da kuma kare mutuncin al’umma.”

Source: Original
Matan da aka kama sun yi nadama
A ɓangaren matan da aka kama, sun amsa cewa suna musayar majazajensu ne bisa umarnin abokan, waɗanda suka gamsar da su cewa yin hakan abu ne na yau da kullum.
Kamar mazajen nasu, su ma matan sun nuna matuƙar nadama tare da roƙon gafara, suna masu alƙawarin ba za su sake komawa ga wannan dabi'a ba, in ji rahoton Leadership.
Hukumar Hisbah ta jaddada matsayarta na yaƙi da dukkan nau'o'in aure na baƙar fata ko dabi'un da suka saɓa wa shari'a da koyarwar addini.
Makwabta sun yi musayar matansu
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu mazaje biyu da ke makwabtaka da juna sun yi musayar matansu da ‘ya’yansu a wani biki da ya bai wa mutane mamaki.
A matsayinsu na makwabta suna kai ziyara ga junansu kafin ziyarar ta rikide ta koma soyayya tsakaninsu, inda kowane miji ke neman matar dayan a sirrance.
Da soyayyar ta fito fili, sai ma’auratan suka yanke hukuncin gyara matsalar ta hanyar musanyan matansu da kuma bikin aure a tsakaninsu don tabbatarwa.
Asali: Legit.ng


