'Yan Bindiga: Yadda Gwamnatin Sokoto Ta Shirya Sayo Baburan Naira Miliyan 2
- Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kashe N1.759bn wajen sayen baburan Bajaj domin rabawa hukumomin tsaro su samu damar yakar yan bindiga
- An ce baburan za su taimaka wajen inganta zirga-zirgar jami’an tsaro a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a sassan Sokoto
- Gwamnatin ta kuma amince da wasu ayyukan ilimi, kiwon lafiya, ruwa da koyar da sana’o’i na sama da Naira biliyan 2 domin inganta rayuwar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da ware N1.759bn domin sayen baburan Bajaj 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga da inganta ayyukan tsaro a faɗin jihar.
An cimma matsayar ne a taron majalisar zartarwar jihar na shida a shekarar 2026, wanda Mataimakin Gwamnan Sokoto, Idris Muhammad Gobir, ya jagoranta.

Source: Facebook
Sanarwar da gwamnati ta wallafa a shafin yanar gizonta ya nuna cewa Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ne ya fitar ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, 2026.
An tasamma yakar yan bindiga a Sokoto
A ruwayar jaridar Punch, gwamnatin ta ce baburan za su ƙara wa motocin sulke 62 da gwamnatin jihar ta saya a baya kan N27bn tare da raba su ga hukumomin tsaro.
Gwamnatin Sokoto ta ce za a yi amfani da baburan ne wajen sauƙaƙa zirga-zirgar jami’an tsaro, musamman a wuraren da ke da wahalar shiga da kuma al’ummomin da hare-haren ’yan bindiga suka fi shafa.
Abubakar Bawa ya ce sayen kayan aikin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin samar wa hukumomin tsaro kayan aiki da za su taimaka musu wajen yaƙi da miyagun laifuka.
Majalisar Sokoto ta yi magana kan tsaro
Ya bayyana cewa majalisar ta jaddada muhimmancin ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro, inda ta ce, an sayi babura 1,000 ne domin ƙara wa motocin sulken da ake da su karfin aiki.
Baya ga batun tsaro, majalisar ta amince da ware Naira miliyan 723.17 domin gyaran Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Runjin Sambo.

Source: Original
Haka kuma, an amince da N498.99m domin gyaran Makarantar Musamman ta A.A. Raji, yayin da aka ware N489.32m domin gyaran mataki na farko na Kwalejin Kimiyyar Jinya.
An kuma amince da N229.36m domin gyaran dakunan kwanan ɗalibai na maza da mata a Kwalejin Nazarin Ilimi na Farko da Gyaran Karatu.
Sojoji sun gwabza da yan bindiga
A wani labarin, mun kawo labarin cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su bayan sun fafata da ƴan bindiga a wata ƙaramar hukuma a Sokoto.
Sojojin sun kuma ƙwato shanu 195, tumaki 84, raƙuma biyu da babura biyu bayan maharan sun tsere sakamakon luguden wutar da aka yi wanda ya firgita su har suka nemi tsira.
Jami'an tsaro sun ce haɗin gwiwar al'umma da bayanan sirri ne suka taimaka wajen samun nasarar wannan samame a yankin tare da bukatar jama'a su ci gaba da samar masu bayanai.
Asali: Legit.ng

