Abin da 'Ubangiji Ya Fada Wa' Shugaban INEC, Amupitan kafin Ya Karbi Tayin Bola Tinubu

Abin da 'Ubangiji Ya Fada Wa' Shugaban INEC, Amupitan kafin Ya Karbi Tayin Bola Tinubu

  • Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya ce ya samu sako kai tsaye daga Ubangiji kafin ya karbi tayin Bola Tinubu
  • Farfesan ya ce ba don wannan sako ba, da ba zai karbi mukamin shugaban hukuma mai muhimmanci kamar INEC ba a Najeriya
  • Joash Amupitan ya ce wannan imani ne ke taimaka masa wajen jure duk wani ƙalubalen da ke tattare da gudanar da zaɓe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa ya amince ya jagoranci hukumar ne bayan samun tabbacin Ubangiji zai taimaka masa a kan aikin.

Farfesa Amupitan, ya ce da bai samu wannan tabbaci ba, da bai karɓi muƙamin shugabancin INEC ba tun farko.

Amupitan
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan yayin ganawa da kwamishinonin zabe a Abuja Hoto: @INECNigeria
Source: Facebook

“Na samu saƙo kai tsaye daga Ubangiji”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Zaben shugaban kasar Najeriya zai yi zafi kamar yaki a 2027

Daily Trust ta ce Amupitan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron godiya da Ƙungiyar Baptist ta Najeriya ta shirya domin karrama shugaban ta mai barin gado, Fasto Israel Akanji da matarsa Victoria.

“Da ban samu wannan tabbaci ba, da ban karɓi aikin ba,” in ji Amupitan.

Ya ƙara da cewa ya samu ƙwarin gwiwa ne daga saƙon da ya ce Ubangiji ya ba shi kafin ya karɓi muƙamin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada shi.

“Ubangiji ya ce kada ka ji tsoro, zan ƙarfafa ka, zan taimake ka, zan riƙe ka. Na ji wannan saƙo a sarari kafin na amince da aikin,” in ji shi.

Abin da ke taimakon Farfesa Amupitan

Shugaban INEC ya ce wannan imani ne ke taimaka masa wajen jure duk wani ƙalubalen da ke tattare da gudanar da zaɓe a ƙasa mai bin tafarkin dimokuraɗiyya kamar Najeriya.

Amupitan ya bayyana cewa jagorancin Allah ne ke ba shi ƙarfi gwiwa a duk lokacin da aka fuskanci matsala, cewar Vanguard.'

“Ko da wane irin ƙalubale ne, Allah yana da ikon kwantar da shi, ya ba mu mafita," in ji shi.

Kara karanta wannan

"Kada ku bar Turawa su yaudare ku": Gumi ya shawarci gwamnati kan sulhu da ƴan ta'adda

Inec.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Amupitan ya buƙaci addu’a kafin zaɓen 2027

Amupitan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa ƙasa da hukumar zaɓe addu’a domin samun nasarar gudanar da zaɓen 2027, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa zaɓen na gaba na iya zama mafi inganci a tarihin ƙasar.

“Ku ci gaba da yi mana addu’a domin zaɓen 2027 ya zama mafi kyau. Ba zan iya yin hakan ni kaɗai ba, amma tare da taimakon Allah, hakan zai yiwu,” in ji shi.

INEC ta matsar da zaben Osun

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da sauye-sauye a jadawalin zaɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa a wannan shekara.

Hukumar INEC ta tunatar da jama'a cewa an riga an ɗan matsa da ranar zaɓen jihar ta Osun da mako guda, don haka an samu sauyi a wa'adin gudanar da kamfe.

INEC ta bayyana cewa wannan sauyi ya zama dole ne domin yin daidai da tanadin sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2026 da shugaban kasa ya sa wa hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262