Bayan Shigar Kwankwaso da Obi, Jagoran NDC Ya Fadi Matsayar Rajistar Jam'iyyar

Bayan Shigar Kwankwaso da Obi, Jagoran NDC Ya Fadi Matsayar Rajistar Jam'iyyar

  • Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya warware zare da abawa kan batun sahihancin rajistar jam'iyyar
  • Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa dole ne dama a rika yada farfaganda kan jam'iyyun da aka ga suna da tasiri
  • Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya bayyana cewa tun da dadewa aka fara kokarin yi wa jam'iyyar NDC rajista

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Henry Seriake Dickson, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da abin da ya bayyana da farfaganda game da jam’iyyar NDC.

Sanata Seriake Dickson ya jaddada cewa tsarin rajistar jam’iyyar yana da daɗaɗɗen tarihi wanda aka rubuta.

NDC na samun karbuwa a Najeriya
Sanata Seriake Dickson na jawabi a wajen tarbar Kwankwaso da Peter Obi zuwa NDC Hoto: @iamHSDickson
Source: Twitter

Dickson ya bayar da wannan ƙarin hasken ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Shugaban NDC a Kano ya fara tutsu, ya zargi Kwankwaso da ƙoƙarin ƙwace masu jam'iyya

NDC na samun karbuwa

Tsohon gwamnan ya kuma sake jaddada kwarin gwiwa kan yadda goyon bayan jam’iyyar yake ƙaruwa a faɗin ƙasar.

Ya ce jam’iyyar NDC tana ci gaba da samun karɓuwa ne saboda abin da ya kira haɗuwar ƴan siyasa masu tasiri da gogewa, waɗanda ke aiki tare don gina dandamalin ƙasa.

A cewarsa, ana gina jam’iyyar ne a matsayin wata tafiya ta siyasa mai akida, wadda aka tsara don ta dore ko bayan waɗanda suka kafa ta babu su, kuma ta kasance tsayayyiya.

“Manufarmu a NDC ita ce mu gina jam’iyyar siyasa mai akida wadda za ta dore fiye da waɗanda suka kafa ta har zuwa ga tsararraki masu zuwa."

- Seriake Dickson

Dickson ya kuma ce jam’iyyar NDC tana ba wa matasa da mata muhimmanci, inda ya siffanta ta a matsayin dandamalin da ke ba wa horarwa, sanya kowa a cikin harkoki, da kuma hidimar al’umma fifiko.

Batun rajistar jam'iyyar NDC

Kara karanta wannan

APC ko ADC: Gwamna Makindee ya fadi jam'iyyar da za ta samar da shugaban kasa a 2027

Yayin da yake bayanin tsarin kafuwar jam’iyyar, ya bayyana cewa takardu sun nuna cewa an fara tsarin rajistar NDC ne tun a shekarar 2017, inda aka ce hukumar INEC ta bayar da amincewar farko kafin daga baya aka dakatar da shi.

Ya ƙara da cewa lokacin da aka ci gaba da rajistar jam’iyyun siyasa a shekarar da ta gabata, masu kokarin yi mata rajista sun sake duba tare da sabunta buƙatarsu ta baya domin ta yi daidai da buƙatun yanzu.

“Don tarihi, lokacin da aka ci gaba da rajistar jam’iyyu a shekarar da ta gabata, mun sake duba tare da sabunta buƙatarmu ta farko."

- Seriake Dickson

Dickson ya kare rajistar jam'iyyar NDC
Sanata Seriake Dickson tare da Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi Hoto: @iamHSDickson
Source: Twitter

An fara rajistar NDC a 2017

Haka kuma Dickson ya yi nuni da rubutattun bayanai, waɗanda suka haɗa da bayanan shirye-shirye na shekarar 2017, waɗanda ya ce suna daga cikin tarihin jam’iyyar da aka rubuta.

Duk da haka, ya amince cewa irin waɗannan yunƙurin siyasa galibi suna fuskantar suka da kuma karkatattun bayanai, inda ya buƙaci magoya baya da ƴan Najeriya da su ci gaba da mayar da hankali.

Kwankwaso ya aika sako ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aika sako ga 'yan Najeriya bayan sauya shekarsa zuwa NDC.

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci magoya bayansa da su yi rajista da jam’iyyar NDC wadda ya sauya sheka zuwa cikinta bayan ficewa daga ADC.

Kwankwaso wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta iya ceto ’yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng