Wike Ya Yi Magana bayan Hukuncin Kotun Koli kan Rikicin Shugabancin PDP, ADC
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani bayan Kotun Koli ta yi hukunci game da rikicin shugabancin PDP da ADC
- Wike ya ce hukuncin Kotun Koli ya kawo ƙarshen rikicin cikin PDP, yana tabbatar da cewa jam’iyyar yanzu tana da shugabanci guda ɗaya kacal
- Tsohon sanatan ya nanata cewa taron Ibadan da ya samar da shugabancin Tanimu Turaki ya sabawa umarnin kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da hukuncin Kotun Koli kan rikicin PDP.
Wike ya bayyana cewa yanzu babu sauran rikici ko ɓangarori a cikin jam’iyyar PDP bayan hukuncin Kotun Koli wanda aka yi a yau Alhamis 30 ga watan Afrilun 2026.

Source: Facebook
Ya yi wannan bayani ne a gidansa da ke Abuja jim kaɗan bayan kotun ta yanke hukunci, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Abin da Wike ya ce kan hukuncin Kotun koli
Wike ya shaida wa manema labarai cewa hukuncin Kotun Koli ya tabbatar da cewa PDP jam’iyya guda ɗaya ce kawai.
Ya ce yanzu babu wanda zai sake magana kan wani ɓangare ko rikici a cikin jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya.
Kotun Koli ta soke babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a Ibadan tsakanin ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamban 2025.
Wannan taro ne da ya samar da shugabannin da Tanimu Turaki ke jagoranta a lokacin rikicin shugabanci.
Kotun ta bayyana cewa an gudanar da taron ne cikin rashin biyayya ga umarnin kotu, lamarin da ya zama cin zarafin tsarin shari’a.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar PDP.

Source: Facebook
Wike ya magantu kan makomar bangaren Turaki
Wike ya kuma yi magana kan makomar masu goyon bayan ɓangaren Turaki, ciki har da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.
Rahotanni daga shafin Punch suka ce Wike ya ce bai san inda za su dosa ba bayan hukuncin kotun.
Ministan ya sake jaddada cewa taron da ɓangaren Abdulrahman Mohammed ya gudanar a watan Maris 2026 ne kaɗai yake da inganci.
Wannan taro da magoya bayan Wike suka mara wa baya ya sake zaɓen shugabannin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.
Wike ya kuma bayyana cewa ba za su karɓi mutanen da ke tare da Atiku Abubakar a cikin ADC zuwa PDP ba.
Ya ce waɗannan mutane ba kadarar siyasa ba ne, illa ma matsala ga nasarar zaɓe a gaba wanda hakan zai jawo cikas a kasar.
Kotu ta yi hukunci kan rikicin ADC
Mun ba ku labarin cewa komai ya zo karshe bayan Kotun Koli a Najeriya ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark a matsayin shugaban ADC na kasa.
Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Mohammed Lawal Garba ya soke umarnin kotun daukaka kara na a tsaya inda ake.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi martani tare da yin maraba da wannan hukunci, yana mai cewa akwai sauran aiki a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

