Ficewar Obi, Kwankwaso Ya Jawo Farraka a Gefen Adawa kan Tsayar da Dan Takara 1
- Yayin da jam'iyyun adawa ke shirin tsayar da dan takara daya a zaben 2027, rikici ya kara tsananta a tsakaninsu saboda wasu sauye-sauye
- Hakan na da nasaba da ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga ADC zuwa NDC gabanin zaben shugaban kasa na 2027
- Magoya bayan Atiku Abubakar sun ce shirin tsayar da dan takara daya tilo domin kalubalantar Bola Tinubu a 2027 yana nan daram
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sababbin rikice-rikice sun kunno kai a cikin hadakar jam’iyyun adawa yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga ADC zuwa NDC.

Source: Twitter
Makusantan Atiku Abubakar, sun bayyana cewa shirin tsayar da dan takara daya tilo domin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai rushe ba duk da sabbin sauye-sauyen siyasa, cewar Punch.
Dalilin barin Kwankwaso, Obi na barin ADC
Atiku, wanda ya fice daga PDP a shekarar 2025, ya shiga ADC ne domin hada kan jam’iyyun adawa kafin Obi da Kwankwaso su biyo baya a 2026.
Sai dai rikice-rikicen siyasa sun sa Obi da Kwankwaso suka fice daga ADC, lamarin da ya bar Atiku cikin wani mawuyacin yanayi a cikin hadakar siyasar.
Wata majiya daga bangaren Atiku ta bayyana cewa batun ko zai yi wa’adi daya kacal idan ya samu tikitin takara bai kamata a fara tattaunawa kansa yanzu ba.
Majiyar ta ce a yanzu Atiku ya fi mayar da hankali wajen ganin ADC ta bunkasa kuma ta zama jam’iyya mai karfi kafin a fara maganar wasu sharudda.
Ya kwatanta ADC da jirgin kasa inda wasu ke sauka wasu kuma ke shiga, yana mai cewa ficewar Obi da Kwankwaso ba zai hana wasu shiga jam’iyyar ba.
Sai dai wasu manyan jam’iyyun adawa sun yi watsi da batun tsayar da dan takara daya tilo, abin da ke nuna karin rabuwar kai a tsakanin su.
Jagoran NDC, Seriake Dickson, ya ce lokaci bai yi ba da za a fara tattauna batun tsayar da dan takara daya domin zaben 2027.

Source: Facebook
Matsayar wasu jam'iyyun adawa
Shi ma shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babban burin jam’iyyun adawa shi ne kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar hadaka ko kowace hanya ta doka.
Wani bangare na ADC karkashin Nafiu Bala Gombe ya ce jam’iyyar ba ta goyi bayan duk wata yarjejeniya da aka cimma a taron Ibadan ba.
Jam’iyyar LP ita ma ta ce a yanzu hankalinta yana kan gudanar da babban taronta na kasa kafin ta fara tunanin hadakar siyasa, cewar Daily Post.
A gefe guda, magoya bayan Obi da Kwankwaso suna matsa lamba a bar kujerar shugaban kasa a Kudu domin tabbatar da daidaito da adalci.
NDC ta sasanta rikicin siyasa a Kano
A wani labarin, an ji cewa jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta warware rikicin shugabanci a Kano, bayan wasu kalamai da ake ganin ba su dace ba.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Hon Mai Riga ya fito kafafen yada labarai yana zargin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo NDC da mutanensa kuma za a tura su gefe.
Ya ce ba za su taba lamunta ba a yi masu abin da ya kira ture kaza kwashe kwai gabanin zaben 2027 ba kafin daga bisani a sasanta su.
Asali: Legit.ng

