Pantami zai Yi Yaki da Zalunci wajen Fitar da Dan Takarar Gwamnan APC a Gombe

Pantami zai Yi Yaki da Zalunci wajen Fitar da Dan Takarar Gwamnan APC a Gombe

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya fito ya yi magana kan fitar da dan takara da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta a jihar Gombe
  • A wani zama da masu ruwa da tsaki na APC a gidan gwamnatin jihar Gombe, an sanar da Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takara
  • A martanin da ya yi kan lamarin, Sheikh Pantami ya nuna cewa ba a bi ka'ida ba wajen fitar da dan takarar kuma zai kalubalanci hakan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Tsohon ministan sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin haske kan fitar da 'yan takara da APC ta yi a jihar Gombe.

Malamin ya yi magana ne bayan shgabannin APC na jihar, karkashin jagorancin gwamna Inuwa Yahaya sun zabi Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Sheikh Isa Ali Pantami a Abuja
Sheikh Isa Ali Pantami yayin wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A wata hira da BBC Hausa ta wallafa a Facebook, Sheikh Pantami ya sanar da cewa zai kalubalanci matakin saboda babu adalci a cikinsa.

Korafin Pantami kan APC

Pantami ya bayyana cewa ba a yi ittifaki ba wajen fitar da dan takarar gwamna a Gombe kamar yadda dokar kasa ta tanada, ya ce kafin a fitar da dan takara ta sulhu sai an cika sharuda uku.

Ya bayyana cewa dole a samu yardar cewa dukkan masu neman takara sun hakura, kuma dukkansu sun shiga tattaunawar da aka yi da kuma tabbatar da an bi doka.

A karkashin haka, Sheikh Pantami ya ce hanyar da aka bi wajen fitar da dankarar ba ta cika ko daya daga cikin sharuda uku da ya ambata ba.

Zaman Inuwa Yahaya da 'yan takara

Game da zama da 'yan takara da aka yi, Pantami ya bayyana cewa gwamna ya yi alkawarin cewa zai yi adalci a tattaunawa da suka yi.

Kara karanta wannan

2027: APC ta kwantar da hankalin Pantami, ta ba shi dama kan batun takarar gwamna a Gombe

Pantami ya sanar da cewa bayan gwamna ya ce za a yi adalci, ya nemi a bi matakin sulhu wajen fitar da 'yan takara, idan kuma ba a cimma matsaya ba sai a yi 'yar tike.

Ya kara da cewa sun samu gayyata a kurarren lokaci kan zama na biyu da aka sanar za a yi saboda haka ne ba su samu halarta ba.

Ya kuma bayyana cewa bai samu sanarwa ba kan yadda aka fitar da dan takara, shi ma a midiya ya ji labari kamar sauran mutane.

Isa Ali Pantami da 'ya APC a Gombe
Lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami ya sabunta katin jam'iyyar APC a Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Twitter

Pantami zai yaki zalunci a Gombe

Sheikh Pantami ya bayyana cewa zai cigaba da fada da zalunci a harkar fitar da dan takara ko da shi aka marawa baya ta hanyar da bata dace ba.

Ya bayyana cewa zai yaki zalunci wajen tabbatar da na yi 'yar tike wajen fitar da dan takarar gwamnan APC a jihar Gombe.

Sai dai ya bayyana cewa babban kalubale kan 'yar tike shi ne:

"Shin na adalci za ko na zalunci za a yi, in na adalci ne, to albishirinmu, jam'iyyarmu da izinin Allah za ta yi nasara, in na zalunci ne, hatsari ya faru, to kowa zai rasa al'amarin zai lalace, don Allah bai taba goyon bayan zalunci ba, kuma zaluncin nan, ko ni aka ba wa zalunci Allah ba zai barni ba."

Kara karanta wannan

Bayan Pantami, Goje da Sanata Alkali sun yi watsi da 'yan takarar APC a Gombe

Ga bidiyon hirar da aka yi da Pantami a kasa:

Korafin Goje kan APC a Gombe

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Muhammadu Danjuma Goje ya yi watsi da hanyar da aka bi wajen fitar da 'yan takara a Gombe.

Sanata Goje ya bayyana cewa matakan da aka bi ba su cika sharudan da dokar kasa ta tanada ba, kuma bai amince da shi ba sam-sam.

A daya bangaren, Saidu Ahmed Alkali da ke neman takarar gwamna a APC ya bayyana cewa matakan da aka bi wajen fitar da 'yan takara ba su cika sharuda ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng