Abba Ya Kinkimo Aiki, Za a Kashe sama da N21bn don Jiƙa Kanawa da Ruwan Sha

Abba Ya Kinkimo Aiki, Za a Kashe sama da N21bn don Jiƙa Kanawa da Ruwan Sha

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe Naira biliyan 21.29 domin gyaran manyan cibiyoyin ruwa a Kano
  • Ayyukan sun shafi na Tamburawa, Challawa da Goron Dutse domin dawo da samar da ruwa wanda ake fama da karancinsa a jihar
  • Gwamnati ta bayyana ɗaukar wannan mataki ne a lokacin da mutanen Kano a birni da karkara ke kuka da ƙarancin ruwan sha

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano, ta hannun ma’aikatar albarkatun ruwa, ta sanar da cewa Mai girma gwamna, Abba Kabir Yusuf ya dauko manyan ayyuka a ɓangaren ruwan sama.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe kimanin Naira biliyan 21.29 domin gyara da farfado da muhimman cibiyoyin samar da ruwa a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tuna da mutanen da hare hare suka shafa a Plateau, ya ba da tallafin kudi

Kano za ta gyara matatun tace ruwan sha
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da tawagar zagaye zuwa matatar Challawa a karamar hukumar Kumbotso da ke Kano Hoto: Abubakar Lecturer/Abba is working
Source: Facebook

Mukaddashin kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da Ibrahim Adam ya wallafa a shafin Facebook.

Gwamnatin jihar Kano ta dauko aikin ruwa

Daily Nigerian ta wallafa cewa a cikin sanarwar, Mukaddashin kwamishinan ya ce wannan mataki ya zo ne domin magance matsalar karancin ruwa da ta dade tana addabar al’ummar Kano.

Ya ce ayyukan za su mayar da hankali kan manyan cibiyoyin da suka lalace, lamarin da ya janyo raguwar samar da ruwa a matakin da ya kamata.

Ayyukan da aka amince da su sun hada da gyaran cibiyar tace ruwa ta Tamburawa da kuma dawo da aikin tashar ta ce ruwan famfo kan kudi Naira biliyan 9.9.

Gwamnatin Kano za ta kashe sama da N21M a bangaren ruwa
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da tawagar zagaye zuwa matatar Challawa a karamar hukumar Kumbotso da ke Kano Hoto: Abubakar Lecturer
Source: Facebook

Haka kuma za a gyara tashar famfon gyaran ruwan a Challawa da cibiyar tace ruwa, tare da dawo da aikin rumbunan ajiyar ruwa na Goron Dutse kan kudi Naira biliyan 11.39.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dauko batun nada Murtala Garo mataimakinsa, ya fadi dalilin ba shi mukami

Dakta Hashim ya bayyana cewa wannan na daga cikin manyan ayyukan a bangaren ruwa a ‘yan shekarun nan, yana mai jaddada cewa aikin yana da matukar muhimmanci da gaggawa.

Yadda za a farfaɗo da ruwan sha a Kano

A cewarsa, cibiyar Tamburawa wacce aka tsara ta rika samar da lita miliyan 150 na ruwa a rana, a halin yanzu tana aiki ne da kusan 27% kacal sakamakon lalacewar da ambaliya ta jawo a 2022.

Hakazalika, cibiyar Challawa mai karfin samar da lita miliyan 220 a rana, ita ma tana aiki ne da kasa da 30% kawai.

Ya kara da cewa an samar da cibiyoyin biyu domin samar da lita miliyan 370 a kullum, amma yanzu ba da ita aikin da aka tsara su a kai wanda ya jawo ƙarancin ruwa.

Gwamnatin Kano ta ce waɗannan manyan ayyuka da aka dauko za su taimaka wajen wadata Kano da ruwa yadda ya kamata.

Abba ya magantu kan Mataimakin gwamnan Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kare matakin da ya dauka na nada Hon. Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48

Kalaman nasa na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da nadin da aka yi wa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna.

Gwamna Abba ya bayyana cewa Murtala Sule Garo ya cancanci mukamin da aka ba shi domin mutum ne da zai iya ba da gudunmawar da ta dace don ci gaban jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng