Badakalar PFIPC: Adeniyi Ya Yi Sabuwar Fallasa yayin da Yake Tsare a Hannun 'Yan Sanda
- Adeniyi Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun amince ko sun yi hulɗa da hukumar da ake takaddama a kanta
- Lauyoyinsa sun buƙaci a ba shi damar bayyana gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke bincike kan badakalar PFIPC
- Sun ce fitar da rahoto ba tare da sauraron Adeyemi ba zai saɓa wa haƙƙinsa na samun adalci a binciken da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja - Adeniyi Adeyemi, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban hukumar PFIPC ya musanta zargin cewa shi kaɗai ya ƙirƙiri hukumar da ake takaddama a kanta.
Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya sun gudanar da ayyuka, sun amince ko kuma sun yi hulɗa da hukumar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tawagar lauyoyinsa ta fitar ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2026.
Adeyemi ya kuma buƙaci a ba shi damar bayyana gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken hukumar.
Festus Akhigbe ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin tawagar lauyoyin Adeyemi, wanda yanzu haka yake tsare a hannun ‘yan sanda.
Lauyoyi sun nemi a saurare shi
Tawagar lauyoyin ta ce ya kamata a ba Adeyemi damar ba da shaida a gaban kwamitin da Yusuf Gagdi ke jagoranta.
Sun yi gargaɗin cewa duk rahoton da za a fitar ba tare da sauraron Adeyemi kai tsaye ba zai saɓa wa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki na samun adalci.
Sanarwar ta ce:
“A hukumance muna buƙatar kwamitin ya bayar da amincewar da ta dace domin a ba wanda muke karewa, Prince Adeniyi Adeyemi Matthew, damar bayyana da kansa tare da ba da shaida.”
“Duk sakamakon bincike ko rahoton ƙarshe na Majalisar Dokoki da aka fitar ba tare da ba wanda muke karewa damar a saurare shi kai tsaye ba, zai kasance mai manyan kura-kurai, bai cika ba, kuma ya saɓa wa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki na samun adalci.”
Zargin ware Adeyemi shi kaɗai
Lauyoyin Adeyemi sun ƙi amincewa da abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin nuna wanda suke karewa a matsayin “mai shirya zamba shi kaɗai” da ya ƙirƙiri wata hukumar gwamnati ba tare da goyon bayan hukumomi ba.
A cewar sanarwar, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya amince da wasu takardu da suka shafi hukumar, tare da taimakawa wajen ware mata ofishi a Babbar Sakatariyar Tarayya.
Haka kuma, an ce Ofishin Akanta Janar na Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) sun yi aiki bisa takardun hukuma wajen samar da lambobin kasafi na gudanarwa da ba hukumar damar kula da asusunta da kanta.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumomin sun tura ma’aikatan gwamnatin tarayya zuwa hukumar tare da buɗe mata asusun gudanar da ayyuka.
An amince da tsarin hukumar
A cewar lauyoyin, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya amince da tsarin kafa hukumar tare da ba da rangwamen da ya ba ta damar ɗaukar ma’aikata 314.
Sun kuma ce shugabannin hukumomin tsaro sun halarci wasu shirye-shiryen da hukumar ta shirya.
Lauyoyin sun ƙara da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta ware wata kadara ga hukumar, ta nemi a biya kuɗin gudanar da aiki, sannan ta bai wa shugabannin hukumar wata lambar yabo ta karramawa.

Source: Facebook
An ce ana mayar da shi saniyar ware
Tawagar lauyoyin ta ce ana ƙoƙarin mayar da Adeyemi “saniyar ware domin a ɓoye manyan kura-kurai na hukumomi, tangardar hanyoyin gudanar da aiki da kuma amincewar da aka bayar a cikin tsarin gwamnati.”
Sun buƙaci a faɗaɗa binciken tare da haɗa ƙungiyoyin farar hula, masana shari’a da masu sa ido masu zaman kansu.
A cewarsu, ya kamata a binciki dukkan takardun da suka danganci hukumar a ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban.
Bincike kan hukumar PFIPC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta bayyana gaban kwamitin da ke bincike kan hukumar PFIPC.
Didi Esther Wilson Jack ta bayar da tabbacin cewa ofishinta ya ba wa hukumar izinin gudanar da aiki ne bisa takardun da aka gabatar masa.
Asali: Legit.ng


