Atiku Ya Goranta wa Obasanjo, Ya Faɗi yadda Arewa Ta Yi Masa Gata a Siyasa

Atiku Ya Goranta wa Obasanjo, Ya Faɗi yadda Arewa Ta Yi Masa Gata a Siyasa

  • Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya yi magana kan tasirin siyasar Olusegun Obasanjo
  • Atiku ya ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da karfin siyasa musamman game da zaben shugaban kasa a 2027
  • Dan takarar ADC ya ce Arewa ce ta taimaka wajen tabbatar da nasarar Obasanjo a 1999, saboda bai samu nasara a jiharsa ko Kudu maso Yamma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake yin magana kan Olusegun Obasanjo.

Atiku ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da karfin siyasa a Najeriya ko kadan.

Atiku ya yi shagube ga Obasanjo
Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: UGC

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai ranar Laraba, amid rahotannin cewa Obasanjo ya ki goyon bayan takararsa, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gargadin da Janar Babangida ya yi wa Obasanjo kan Atiku Abubakar

Atiku ya caccaki tsohon mai gidansa, Obasanjo

Da yake mayar da martani kan matsayin tsohon shugaban kasar, Atiku ya ce bai damu da ko Obasanjo ya goyi bayansa ba.

Ya tuna rawar da ya ce masu kada kuri’a daga Arewa suka taka wajen taimaka wa Obasanjo zama shugaban kasa a shekarar 1999.

Atiku ya ce:

“A shekarar 1999, bai ma iya cin zabe a jiharsa ko Kudu maso Yamma ba; Arewa ce ta mai da shi shugaban kasa.”

Ya kara da cewa Obasanjo ba shi da wata babbar darajar zabe da za ta iya yin tasiri wajen tabbatar da nasarar wani dan takara.

Atiku ya tuna yadda Arewa ta yi wa Obasanjo gata
Dan takarar shugaban ƙasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Atiku da Obasanjo sun yi aiki tare a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, amma dangantakarsu ta siyasa ta samu matsala.

Yadda Atiku Abubakar ya taka wa Obasanjo birki

A baya, Atiku ya bayyana cewa ya yi adawa da yunkurin Obasanjo na neman wa’adi na uku saboda kare kundin tsarin mulki da dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

Da yake magana kan zaben 2027, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana irin damammakin da ya samar wa matasan Najeriya a lokacin mulkinsa.

Atiku ya ce wasu daga cikin matasan da suka amfana da irin wadannan damammaki sun zama gwamnoni, ministoci, daraktoci da sauran masu rike da mukaman gwamnati.

Ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027, zai ci gaba da samar wa matasa damammakin shiga harkokin gwamnati.

Ya ce hakan zai ba matasan Najeriya damar yin aiki da kuma karbar mukaman shugabanci a kasar, cewar Daily Post.

Atiku Zai dawo da tallafin mai

An ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Ya ce gwamnati ta kasa fadin inda kuɗin da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur suka tafi, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da su wajen rage talauci.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai dawo da tallafin tare da ƙwato kuɗin da ya ce an wawure, idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.