Osun: Malamin Addini Ya Shawarci Matasa Su Yi Koyi da Davido a Zaben 2027
- Fasto Eugene Ogu ya yaba wa rawar da mawaki Davido ya taka wajen shiga harkokin zabe da kare dimokuradiyya a Osun
- Ogu ya bayyana damuwa kan yiwuwar gallazawa Davido saboda goyon bayan kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya lashe zaben Osun
- Ya bukaci matasa su kada kuri’a a 2027, su kare kuri’unsu, su bibiyi tattara sakamako, sannan su zabi ’yan takara bisa kwarewa da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Yayin da yakin neman zaben babban zaben 2027 ya fara, fasto ya shawarci matasan Najeriya game da zaben 2027.
Apostle Eugene Ogu ya bukaci matasan Najeriya su yi koyi da yadda mawaki Davido ya shiga harkar zabe a zaben gwamnan Osun na baya-bayan nan.

Source: Twitter
Ogu ya bayyana hakan ne a Port Harcourt, yayin da yake nazarin zaben da aka gudanar a ranar 15 ga watan Agustan 2026, cewar Vanguard.
Ana zargin shirin gallazawa Davido
Ya nuna damuwa kan yiwuwar gallazawa Davido saboda fito-na-fito da ya yi wajen goyon bayan kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya lashe zaben.
Malamin ya yaba wa mawakin saboda abin da ya bayyana a matsayin jarumtaka da kuma taka rawa wajen gudanar da tsarin zabe.
Ya kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da sauran ’yan Najeriya su tabbatar da tsaron lafiyarsa.
Ogu ya kuma yi tambaya kan rahotannin cewa wasu fitattun ’yan Najeriya, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, sun tuntubi Davido yayin zaben tare da neman ya goge wani rubutu da ya wallafa a kafar sada zumunta.
Ogu ya ce kiraye-kirayen da irin wadannan manyan mutane suka yi na iya haifar da manyan illoli.
Ya bukaci ’yan Najeriya da kasashen duniya su binciki yanayin kiran da aka ce an yi wa Davido da kuma rahoton alakar Dangote da zaben Osun.

Source: Twitter
Gargadin da fasto ya yi game da Davido
Sai dai ya yi gargadin cewa bai kamata a dauki wani mataki da zai jefa mawaki Davido ko wasu fitattun mutane da za su iya zama manyan masu magana kan zaben Osun cikin hadari ba.
Ogu ya kuma yi Allah-wadai da tabarbarewar matsin tattalin arziki a Najeriya, inda ya kwatanta halin da ake ciki da Samariya ta Littafi Mai Tsarki, wadda tsananin yunwa ya jefa cikin halin matsananci.
Malamin ya bukaci matasan Najeriya su shiga zaben 2027 sosai ta hanyar kada kuri’a, kare kuri’unsu da kuma bibiyar tsarin tattara sakamako har zuwa lokacin da aka sanar da sakamakon karshe, cewar Punch.
Ya ce abin kunya ne ganin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ake sa ran zai kasance mai kare doka, tare da gwamnoni 19 na APC da ’yan daba na siyasa sun je Osun da makudan kudade domin kokarin karkatar da sakamakon zabe.
'An yi nufin farmakin Davido' - Yan sanda
Mun ba ku labarin cewa yan sanda sun ce maharan da suka kai hari kan ayarin gwamnan Osun sun yi hakan ne domin kai wa fitaccen mawaki Davido hari.
Rundunar ’yan sanda ta ce wani tsohon mai laifi da ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar asiri ta Eye Confraternity ya yi ƙoƙarin isa wurin Davido..
An harbe wani mutum mai shekaru 60, Tajudeen Yusuf, har lahira yayin da ake musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da waɗanda ake zargi da kai hari.
Asali: Legit.ng


