Ghana Ta Naɗa Sheikh Bashir Aliyu Shugaban majalisar Banki Marar Kudin Ruwa

Ghana Ta Naɗa Sheikh Bashir Aliyu Shugaban majalisar Banki Marar Kudin Ruwa

  • Babban Bankin Ghana ya ƙaddamar da Majalisar ba da Shawara kan harkokin banki wanda ba ya dauke da kudin ruwa domin inganta tsarin kuɗin Musulunci a ƙasar
  • Farfesa Bashir Aliyu, malamin addinin Musulunci kuma masani kan Shari’a daga Najeriya ne wanda bankin ya naɗa shugaban majalisa
  • Majalisar za ta taimaka wa Babban Bankin Ghana wajen tsara dokoki da sa ido kan bankuna da cibiyoyin kuɗi masu aiki ba tare da tsarin riba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ghana – Babban Bankin Ghana ya kafa wata sabuwar Majalisar ba da shawara kan harkokin banki da sauran hada-hadar kuɗi nara ruwa, wato NIFAC domin bayar da gudunmawa wajen haɓaka tsarin banki na tsarin Musulunci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

Majalisar za ta kasance wata muhimmiyar hanyar ba da shawarwari ga bankin kan yadda za a tafiyar da, kula da kuma sa ido kan cibiyoyin kuɗi da ke amfani da tsarin banki marar riba.

Sheikh Bashir Aliyu ya samu mukami a Ghana
Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Bashir Aliyu Hoto: Dr. Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Wannan na cikin sakon da bankin ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka nada Malamin a kan wannan mukami.

Ghana: Dalilin kaddamar da kwamitin bankin Musulunci

BBC ta wallafa cewa kaddamar da majalisar na daga cikin matakan da Ghana ke ɗauka domin ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi da ya dace da ƙa’idojin Shari’ar Musulunci, tare da tabbatar da cewa masu amfani da irin waɗannan ayyuka sun samu kariya da amincewa da tsarin.

A lokacin bikin ƙaddamar da majalisar da aka gudanar a wannan mako, Gwamnan Babban Bankin Ghana, Dakta Johnson Asiama, ya bayyana muhimmancin samar da ingantaccen tsarin tafiyar da harkokin banki marasa riba.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Ya ce akwai buƙatar a tabbatar da cewa tsarin yana aiki cikin gaskiya da ƙwarewa, tare da kare haƙƙin masu amfani da ayyukan bankunan da kuma samar da yanayin da zai sa jama’a su amince da tsarin.

Ghana: Sheikh Bashir Aliyu ya samu mukami

Babban Bankin Ghana ya naɗa fitaccen malamin addinin Musulunci daga Najeriya, Farfesa Bashir Aliyu, a matsayin shugaban majalisar.

Farfesa Bashir malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma yana daga cikin masana da suka yi fice a fannin Shari’ar Musulunci da harkokin kuɗi.

Ana son malamin zai taimaka wajen tabbatar da an bi tsarin Musulunci
Farfesa Bashir Aliyu, Malamin addinin Musulunci Hoto: Dr. Bashir Aliyu
Source: Facebook

Haka kuma, shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Shari’a a Najeriya (SCSN), wadda ke taka rawa wajen shawarwari da nazarin al’amuran da suka shafi Shari’ar Musulunci.

Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Dakta Yussuf Adany Al-Badani, Dakta George Baah-Danquah, Adishetu Hamidu Naabo da Samuel.

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya ta aiko saƙo Najeriya bayan APC ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun

Ƙirƙirar majalisar na nuni da ƙoƙarin Ghana na faɗaɗa hanyoyin hada-hadar kuɗi da kuma samar da tsarin banki da zai iya biyan buƙatun al’umma masu neman ayyukan kuɗi marasa amfani da riba.

Raddin Sheikh Bashir ga Tinubu

A baya, kun samu labarin cewa Malamin Musuluncin nan, Dr Bashir Aliyu Umar ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu martani game da rokon da ya yi na neman yan Najeriya su yafe masa.

Malamin ya bayyana cewa babban abin da ya kamata Shugaban kasa ya mayar da hankali a kansa shi ne sauke nauyin da ke kansa na tabbatar da cewa wadanda ya ke jagoranta sun samu abin da ya dace.

A wajen bude tafsirin Ramadan 2026 a fadar shugaban kasa ne Bola Ahmed Tinubu ya roki 'yan Najeriya su yafe masa idan ya masu laifi yayin da ya ke kokarin tabbatar da cewa an gyara kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng