ICPC Ta Dauki Matakai a kan Likitan Nasir El Rufa'i

ICPC Ta Dauki Matakai a kan Likitan Nasir El Rufa'i

  • ICPC tara fara daukar mataki a kan likitan da ke kula da lafiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i
  • Hukumar ta kai karar likitan da take zargi ya ƙirƙiri rahoton ƙarya kan rashin lafiyar Nasir El-Rufai zuwa MDCN
  • Asibitin Kasa da ke Abuja ya ce lafiyar Nasir El-Rufa'i kalau duk da rahoton da likitansa ya fitar bayan ya duba shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Hukumar yaƙi da rashawa (ICPC) ta shigar da ƙara gaban Hukumar Kula da Ayyukan Likitoci da Masu Haƙora ta Najeriya (MDCN).

Hukumar ICPC ta nemi a hukunta Farfesa Bello Abubakar bisa zargin ƙirƙirar rahoton lafiya da aka yi amfani da shi wajen neman belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An gano hanyar da aka kafa ma'aikatar bogi ta PFIPC

Ana tuhumar likitan El-Rufa'i da bayar da bayanan karya
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, gudunar kotu Hoto: Nasir El-Rufa'i/Getty
Source: Twitter

A rahoton da ya kebanta ga jaridar Premium Times, shugaban hukumar ya buƙaci a buɗe bincike kan likitan saboda abin da ya kira saba wa ƙa'idojin aikin likita.

ICPC ta kai karar likitan El-Rufa'i

Takardar koken wacce aka shigar ta bukaci kwamitin ya gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa domin daukan mataki.

MDCN ita ce hukuma mai kula da aikin likitanci a Najeriya, kuma tana da alhakin binciken korafe-korafen ɗabi'ar ƙwararrun likitoci tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan an same su da laifi.

Takardun da aka gani sun nuna cewa MDCN ta karɓi koken ICPC kan Bello Abubakar tun ranar 8 ga Yuli, 2026 kuma ana sa ran Kwamitin Binciken Likitoci zai fara binciken zargin.

An ƙaryata rahoton likitan El-Rufa'i

A cikin rantsuwar da jami'in binciken ICPC, Alex Omamuli, ya yi, ya bayyana cewa El-Rufai ya gabatar da rahoton lafiya mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Yuni, 2026 domin neman beli saboda rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya kayyade sadakin zawarawa zuwa N1,500 a Bauchi? Gaskiya ta fito

Rahoton ya fito ne da tambarin Asibitin Kasa da ke Abuja, inda Bello Abubakar ya sanya hannu yana bayyana cewa ya yi bincike bisa bayanan lafiyar tsohon gwamnan.

ICPC ta kai kara wurin hukumar da ke kula da likitoci
Ginin hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC a Abuja Hoto: ICPC
Source: Twitter

Sai dai hukumar ICPC ta ce ta rubuta wa babban daraktan Asibitin Kasa domin tabbatar da sahihancin rahoton.

A martanin da asibitin ya bayar ranar 18 ga Yuni, 2026 shugabancin asibitin ya ce babu lambar rajistar mara lafiya a rahoton.

Ya kuma ce binciken da aka gudanar a bayanan marasa lafiya bai nuna cewa El-Rufai ya taɓa yin rajista ko karɓar magani a asibitin ba.

Likitan El-Rufa'i ya shiga matsala

A baya, kun samu labarin cewa hukumar yaƙi da rashawa ta shigar da karar zargin aikata laifuffukan kawo takardun asibitin bogi a shari’ar ta da Nasir El-Rufai.

Wanda ake zargin, wato Bello Abubakar, kwararren likitan ciwon daji ne a Babban Asibitin Kasa na Abuja Kuma shi ne likitan da ke duba tsohon gwamnan Kaduna.

Hukumar ta ce likitan ya rubuta takarda ana neman belin El-Rufai alhali ya san bayanan da ke ciki ba gaskiya ba, kamar yadda ake zargi tare da neman a hukunta shi.

Kara karanta wannan

Abin da Abdulsalami ya fadawa shugaban INEC game da APC, PDP, ADC gabanin 2027

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng