Hakeem Baba Ahmad Ya Fadi Abin da Zai Sa Tinubu Ya Fadi Zabe kafin Karfe 4:00
- Shugaban PRP yana ganin cewa za a iya kayar da shugaban kasa mai ci idan har aka gudanar da sahihin zabe
- Hakeem Baba-Ahmed ya yi nuni da sakamakon zaben jihar Osun a matsayin tabbacin cewa ana iya doke APC
- Dr. Baba-Ahmed ya jaddada cewa sahihanci da adalcin hukumar zabe su ne mabuɗin dorewar tsarin dakaraniyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya dage cewa Bola Ahmad Tinubu ba zai zarce a ofis ba.
A ranar Laraba, 19 ga watan Agusta 2026 aka ji Hakeem Baba-Ahmed ya kara yin hasashen faduwar APC idan aka yi zaben kwarai.

Source: UGC
Hakeem Baba-Ahmed ya kai Bola Tinubu kasa
Za a doke APC muddin INEC ta shirya zabe na gaskiya da adalci da babu magudi a cikinsa, dattijon ya shaida wa tashar Channels.
A hira da aka yi da shi a shirin siyasa na gidan talabijin, shugaban na jam’iyyar PRP ya bayyana APC da dodanniya mai cin kan ta.
Duk da jam’iyya mai mulki tana da jihohi fiye da 30 da kuma rinjaye a duk majalisun tarayya, Baba-Ahmed yana hango karshen ta.
Dattijon na Arewa yake cewa abubuwa sun kara muni a karkashen jagorancin Bola Tinubu wanda ya gaji Muhammadu Buhari a 2023.
Izna daga zaben gwamnan jihar Osun
‘Dan siyasar ya ce nasarar Ademola Adeleke a zaben gwamnan jihar Osun ta nuna yin galaba a kan APC a zaben 2027 mai yiwuwa ne.
"Na ga Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun yana magana da izzarsa, hankalinsa kwance.
An tumurmusa APC da kasa a Osun. Ba mu ma ga taron dangi ko wani hadin-kai dmin a doke APC ba. Jam’iyyu sun yi takara da juna, amma aka yi galaba a kan APC.
Mun ma ji labarin cewa akwai yarjejeniya tsakanin Shugaba Tinubu da Gwamna Ademola Adeleke, amma ba mu yadda da wannan ba.
Mun yi imani cewa jam’iyyar Accord mai mulki ta doke APC ne gaba da baya. Babu dalilin da ya sa ba za a iya maimaita wannan a matakin kasa ba.

Source: Getty Images
Game da zaben 2027, Vanguard ta rahoto ya ce kada wanda ya yabi INEC sai sun yi abin kirki a zaben da Bola Tinubu yana cikin masu takara.
Baba-Ahmed a ce yana da tabbacin Shugaba Tinubu zai kai kasa, amma ba tun 12:00 za a gane APC ta fadi ba, watakila sai zuwa karfe 4:00.
A karshe ya ce:
"Ina fata za a yi zabe na gaskiya da adalci. Idan ba haka ba, ina hango babbar barazan ga damukaradiyyar Najeriya."
Wadanda suka taimaki Accord ta doke APC a Osun
Rahotonmu ya nuna Bola Tinubu, David Adeleke wato Davido da wasu mutane sun taimaka wa tazarcen Gwamna Ademola Adeleke a zaben Osun.
Akwai masu ganin cewa shugaban kasa ya bada dama jam'iyyar Accord ta cigaba da mulki, bai hura wuta sai 'dan takaransa ya karbe mulkin jihar ba.
Adeleke ya ci kwa-kwa kafin ya samu tazarce bayan barin PDP a 2025, an iya birne barakar cikin jam’iyyar Accord, ya tsaya takara ya ci zabe.
Asali: Legit.ng

