Gwamnatin Tinubu Ta Tirje, Ta Ki Fitar da Bayanai game da Rancen $5bn daga Abu Dhabi

Gwamnatin Tinubu Ta Tirje, Ta Ki Fitar da Bayanai game da Rancen $5bn daga Abu Dhabi

  • Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta wallafa cikakkun bayanan yadda za ta kashe kudaden rancen da ta karbo daga Abu Dhabi ba
  • Ya ce Majalisar Dokoki ta Kasa ce ta amince da yarjejeniyar, kuma babban manufarta ita ce sake tsara basussukan da ke da tsadar ruwa
  • Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Fitch Ratings sun nuna damuwa kan tsarin rancen, musamman batutuwan da suka shafi bayyana bayana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa\.

FCT Abuja – Ministan Kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na neman gwamnatin tarayya ta bayyana yadda za ta kashe rancen da ta karbo.

Ta ce ba za ta wallafa dukkanin bayanai game da kudaden da ta karba daga wani tsarin samar da kudi na Dala biliyan 5 da First Abu Dhabi Bank ya tsara ba

Kara karanta wannan

Tsohuwar matar yaron El Rufai ta yi magana watanni shekaru 3 mutuwar aurensu

Gwamnati ta ki fitar da bayanai kan rancen Abu Dhabi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Oyedele ya ce an yi wa yarjejeniyar binciken da ya dace, yana mai cewa Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita, kuma an tsara ta ne domin sake tsara basussukan da suka fi tsada.

Gwamnati ta yi magana kan rancen Abu Dhabi

ICIR ta kawo labarin cewa gwamnatin tarayya ta riga ta karbi kusan Dala biliyan 1.5, wanda shi ne kaso na farko na tsarin Dala biliyan 5 da First Abu Dhabi Bank ya tsara.

Hakan ya zo ne duk da damuwar da Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Fitch Ratings suka nuna kan gaskiya da kuma hadurran da ke tattare da irin wannan tsarin samar da kudi.

Gwamnati ta ce majalisar dokoki ta duba tare da amincewa da rancen Abu Dhabi
Wasu daga cikin yan majalisun Najeriya Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da rancen ne a ranar 31 ga Maris, 2026. Ana sa ran za a yi amfani da kudaden farko wajen tallafa wa kasafin kudin 2026, ayyukan more rayuwa da kuma sake tsara wasu basussukan da gwamnati ke biya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan sayar da litar fetur a N200

Da aka tambaye shi ko gwamnati za ta bayyana yadda za ta yi amfani da kudaden da ta karba daga First Abu Dhabi Bank, Oyedele ya ce gwamnati za ta bayyana yadda take kashe kudaden gwamnati, amma bai ga dalilin da ya sa ake ware wannan rancen ana masa kulawa ta musamman ba.

Gwamnatin Tinubu ta turje

Ya kara da cewa babu wanda ya tambayi gwamnati ko za ta wallafa yadda ta kashe kudaden da ta karba daga Bankin Duniya, Eurobond ko Sukuk.

Oyedele ya kuma yi watsi da zargin cewa an gudanar da yarjejeniyar ba tare da bin ka'ida ba, yana mai cewa an gabatar da ita ga Majalisar Dokoki ta Kasa domin amincewa.

Ya ce:

“An amince da rancen ba kawai daga FEC ba, an kai shi Majalisar Dokoki ta Kasa saboda wasu suna kwatanta shi da wasu kasashe inda ake yin irin wannan abu a boye.”

Ministan ya ce gwamnati ta yi nazari mai zurfi kan yarjejeniyar, kuma tana karbar kudaden a matakai domin kauce wa biyan karin kudin da ba dole ba.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan fetur

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce matatar Dangote ba za ta iya fara aiki yadda ya kamata ba idan har ana ci gaba da sayar da fetur kan kasa da N200.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Trump ya kaddamar da sabon salon yaki da Iran

Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin fetur ya haifar da wahala, amma ya taimaka wajen samar da yanayin da masu zuba jari za su yi aiki domin inanta bangaren.

Oyedele ya ce da ba a cire tallafin ba, Najeriya za ta iya fuskantar karancin fetur, yayin da farashinsa zai iya kaiwa N3,000 a kasuwar bayan fage kuma zai daga hankalin yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng