Martanin Jam'iyyar ADC bayan Ta Rasa Kwankwaso da Peter Obi zuwa NDC

Martanin Jam'iyyar ADC bayan Ta Rasa Kwankwaso da Peter Obi zuwa NDC

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta rasa biyu daga cikin manyan jiga-jiganta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
  • Sakataren yada labarai na kasa na ADC ya bayyana cewa tabbas ficewar manyan 'yan siyasar guda biyu koma baya ne a gare su
  • Sai dai, Bolaji Abdullahi ya bayyana amfanin da ficewar tsofaffin 'yan takarar shugaban kasar zai yi wa jam'iyyar ADC

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan ficewar tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi daga jam'iyyar.

Bolaji Abdullahi bayyana ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar a matsayin koma-baya, amma ba babban rauni da zai ruguza ta ba.

ADC ta yi martani kan ficewar Kwankwaso da Obi zuwa NDC
Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark da tambarin jam'iyyar Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Kakakin na ADC ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin Prime Time na tashar Arise tv a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya

Me ADC ta ce kan ficewar Kwankwaso da Obi?

Bolaji Abdullahi ya amince cewa a kashin kansa bai ji daɗin tafiyarsu ba, sai dai ya lura cewa hakan ya zo da wani mataki na sauƙi.

“Tabbas. Ina nufin, a kashin kaina ban ji daɗin tafiyarsu ba. Kuma ba zan iya gaya muku dalili ba, saboda ina da nawa ra’ayin. Ban ji daɗin tafiyarsu ba. Amma ta wata fuskar, mun samu sauƙi."
"Yanzu za mu iya mayar da hankali kan yin abubuwan da ya kamata mu yi ba tare da fuskantar matsin lambar da suke ƙoƙarin sanya mu a ciki ba.”

- Bolaji Abdullahi

Lokacin da aka matsa masa lamba kan ko ya karaya ne sakamakon abin da ya bayyana na gazawar ƙoƙarin haɗa kan ’yan adawa, Bolaji Abdullahi ya yi watsi da wannan batun.

ADC ta amince ta samu koma baya

Ya amince cewa ficewar tasu koma-baya ce, amma ya dage cewa ba babban rauni ba ne ga manufofin ADC.

Kara karanta wannan

Sakon Kwankwaso ga 'yan Najeriya bayan sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC daga ADC

“Shin hakan koma-baya ne? Amsar ita ce eh. Shin rauni ne da zai ruguza jam’iyya? Amsar ita ce a’a. Domin manufofin a bayyane suke. Har yanzu dai suna nan yadda suke."
"Ba mu ɗauke su a matsayin makiyanmu ba. Ba za mu shiga faɗa da su ba; ba makiyanmu ba ne. Muddin dai manufar tana nan a bayyane."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta yi martani kan ficewar Kwankwaso da Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

ADC ta soki Peter Obi

Bolaji Abdullahi ya kuma soki Peter Obi kan abin da ya kira rashin nuna sha’awa ga tsarin akidar jam’iyyar.

Ya bayyana cewa ADC ta shafe watanni tana aiki wajen samar da kundin manufofinta, wanda ya tsara hanyoyin da za ta bi, amma ya yi iƙirarin cewa Obi bai bayar da gudunmawa ko shiga cikin wannan tsarin ba.

Batun rajistar jam'iyyar NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya warware zare da abawa kan rajistar jam'iyyar.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya bayyana cewa ana yada farfaganda da bayanan da ba daidai ba kan jam'iyyar.

Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa tun shekarar 2017 aka fara yunkurin yi wa jam'iyyar NDC rajista a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng