‘Ku Bar Shan Wahala’: Fasto Ya Faɗi Wanda Zai Zama Shugaban Kasa a 2027

‘Ku Bar Shan Wahala’: Fasto Ya Faɗi Wanda Zai Zama Shugaban Kasa a 2027

  • Malamin addinin Kirista, Fasto Enoch Adeboye ya yi hasashe da jan hankali game da zBen shugaban kasa a shekarar 2027
  • Malamin ya bayyana cewa Allah ya riga ya zabi shugaban Najeriya na gaba kafin zaben 2027, yana cewa ikon Allah ya fi karfin siyasa
  • Fasto Adeboye ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a da zaman lafiya yayin da harkokin siyasa ke kara zafi kafin babban zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Limamin cocin Redeemed Christian Church of God, Enoch Adeboye, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Faston ya bayyana cewa Allah ya riga ya kaddara shugaban Najeriya na gaba kafin zaben shekarar 2027.

Fasto ya ja hankalin yan Najeriya kan zaɓen 2027
Fasto Enoch Adeboye yayin gabatar da huduba a coci. Hoto: @PastorEAAdeboye.
Source: Twitter

Ya yi wannan jawabi yayin taron ma’aikatan cocin a Redemption City dake kan hanyar Lagos zuwa Ibadan, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zubar da jinin 'yan Najeriya zai kawo karshen Tinubu a 2027

Fasto ya shawarci yan Najeriya kan zaɓe

Adeboye ya ce sakamakon zabe ba abu ne da mutane kadai za su iya tantancewa ba, domin nufin Allah shi ne zai tabbata a karshe.

Ya bukaci ‘yan Najeriya su guji fargaba kan siyasa tare da ci gaba da addu’a domin zaman lafiyar kasa.

Malamin addinin ya bayyana cewa bai taba hana Kiristoci shiga siyasa ba, amma dole mutane su fahimci cewa Allah ne ke da ikon karshe a harkokin rayuwar bil’adama ya kara da cewa mutane su yi abin da ya dace sannan su dogara ga Allah.

Fasto Adeboye ya kuma mayar da martani kan kalaman Fasto Isaac Omolehin wanda ya kira shi da Bishop David Oyedepo da Fasto William Kumuyi iyayen Kiristocin Najeriya.

Fasto ya yi hasashe kan zaben shugaban kasa a Najeriya
Babban malamin addinin Kirista a Najeriya, Enoch Adeboye. Hoto: @PastorEAAdeboye.
Source: Twitter

Adeboye ya magantu kan shugabancin kungiyar CAN

Ya bayyana cewa shugaban kungiyar CAN ne kadai yake jagorantar Kiristoci gaba daya a Najeriya, yayin da shi kuma yake gamsuwa da kasancewa shugaban cocin RCCG kawai.

Kara karanta wannan

'Me ka tsinana a shekaru 4': Malamin addini ya kalubalanci tazarcen Tinubu

Ya ce wannan aiki kadai ya isa gare shi kuma bai neman karin nauyi inda kuma yi watsi da rade-radin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa RCCG reshen jam’iyyar APC ce.

Ya ce cocin na ci gaba da magana kan matsalolin da suke damun ‘yan Najeriya musamman matsin tattalin arziki, cewar rahoton TheCable.

Adeboye ya kara da cewa idan kungiyar CAN ta shirya zanga-zangar lumana kan matsalolin shugabanci, zai shiga domin nuna goyon baya.

Ya tuna cewa ya taba shiga irin wannan zanga-zanga lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Ya bayyana cewa ‘yan siyasa suna da damar zuwa tarukan ibada a sansanin cocin, amma ba za a bari su yi amfani da mumbari wajen yakin neman zabe ko tallata siyasa ba.

Barazanar Amurka: Fasto ya ba Tinubu shawara

An ji cewa Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa tun da aka fara kashe kiristoci a Najeriya, ya ankarar da shugabannin kasar don daukar mataki.

Babban limamin cocin RCCG ya shawarci Shugaba Tinubu ya dauki matakan gaggawa tun kafin Amurka ta fara kawo hari.

A cewarsa, ya kamata Tinubu ya ba hafsoshin tsaro wa'adin watanni uku su kawar da yan ta'adda ko kuma su yi murabus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.