INEC Ta Shirya Yin Zabe a Kano da Wasu Jihohi 5 a Watan Yuni

INEC Ta Shirya Yin Zabe a Kano da Wasu Jihohi 5 a Watan Yuni

  • Hukumar zabe ai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanya ranar 20 ga Yunin 2026 domin zaɓukan cike gurbi na majalisa a jihohi shida
  • INEC ta sanar da cewa zaben zai shafi jihohin Kano, Nasarawa da sauransu, inda ta jaddada ana cigaba da shirye-shirye domin yin adalci
  • Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da sabuwar kwamishinar INEC a Abuja ranar Alhamis

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, domin gudanar da zaɓukan cike gurbi a Kano da wasu jihohi shida.

Shugaban hukumar zabe, Farfesa Joash Amupitan ne ya sanar da hakan a wani biki da aka gudanar a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Da gaske an kona gidan Nafiu Bala a Gombe? an samu gaskiya

Shugaban hukumar INEC a Najeriya
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan a ofis. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Legit Hausa ta rahoto cewa INEC ta yi bayani kan zaben ne yayin maraba da sabuwar kwamishinar zabe Jamila Malafa, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Jihohin 6 da za a yi zabe a Yuni

Rahotanni sun nuna cewa INEC ta ce za a gudanar da zaɓukan cike gurbin tare da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka tsara a rana guda.

A INEC, zaɓukan za su haɗa da kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, da kuma kujera ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi da kujera ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano.

Amupitan ya ce:

“Za mu yi wasu zaɓukan da ba su dace da jadawalin yau da kullum ba nan ba da jimawa ba. An tsara zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 20 ga Yuni, 2026. A ranar guda, hukumar za ta gudanar da zaɓukan cike gurbi.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umarni kan jami'in DSS da ake zargi ya sace budurwa a Jigawa

“Za a cike kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, tare da kujera ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi da kuma kujera ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano,”

An nada sabuwar kwamishinar INEC

Da yake magana kan nadin sabuwar kwamishinar INEC, Farfesa Amupitan ya bayyana Rear Admiral Jamila Malafa (mai ritaya) a matsayin ƙwararriya mai kwarewa sosai a harkokin aikin soja da kuma gudanar da zaɓe.

Ya ce ta taba aiki da hukumar a bangaren jigilar kayayyaki, sannan ta rike mukamin Daraktar Harkokin Shari’a a Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, inda ta samu gogewa mai yawa a harkokin gudanarwa da shari’a.

Yadda aka yi zaben Abuja a 2026
Ana kada kuri'a a zaben cike gurbi a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Shugaban ya sake jaddada kudirin hukumar na bin kundin tsarin mulki, inda Vanguard ta rahoto ya ce:

“Nauyin da ke kan mu a bayyane yake. Mun kuduri aniyar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, Majalisar Tarayya, gwamnoni, Majalisun Jihohi da kuma na ƙananan hukumomi cikin gaskiya da adalci,”

Ana so INEC ta soke rajistar ADC

A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiya ta shigar da hukumar INEC, ministan shari'a, Lateef Fagbemi da wasu jam'iyyun siyasa kara.

Kara karanta wannan

Tirkashi: EFCC ta fara farautar babbar jagora a kungiyar yakin neman zaben Tinubu

Kungiyar ta bukaci babbar kotun tarayya ta soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu kananan jam'iyyun siyasa a Najeriya kafin zaben 2027.

A daya bangaren, an samu rahotanni da suka nuna cewa Lateef Fagbemi ya goyi bayan karar da aka shigar, yana cewa jam'iyyun ba su cika sharuda ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng