Mai Son Takarar Gwamna a APC Ya Ki Yarda da Zabin Tinubu, Ya Yi Barazanar zuwa Kotu
- Rigima na neman kunnowa a jam'iyyar APC kan takarar Gwamnan jihar Legas a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Daya daga cikin masu neman takarar a karkashin inuwar APC, Samuel Ajose, ya yi barazanar daukar matakin shari'a
- Samuel Ajose ya yi barazanar ne bayan an yada cewa ya amince da takarar Obafemi Hamzat a inuwar APC don zaben 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Mai neman takarar gwamnan jihar Legas a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Samuel Ajose, ya yi martani kan batun cewa ya amince da takarar Obafemi Hamzat.
Samuel Ajose ya yi watsi da wata sanarwar da ke yawo da ke iƙirarin cewa ya amince da Mataimakin gwamna, Obafemi Hamzat, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Legas na jam’iyyar APC.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo da Samuel Ajose wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Rikicin PDP: Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar shugabancin jam'iyyar a Najeriya
Ajose ya ki goyon bayan matsayar APC
Samuel Ajose ya bayyana sanarwar da ke yawo a matsayin ƙarya kuma wadda ba shi ya bayar da ita ba.
Ya ce rubutun, wanda kuma ya nuna goyon bayansa ga matakin da Majalisar GOC mai ba da shawara kan shugabanci ta jihar Legas (GAC), ba daga gare shi ko ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa ya fito ba.
“Hankalina ya karkata ga yaɗuwar wata sanarwa ta ƙarya kuma mara tushe a kafofin yaɗa labaran Najeriya, wadda ke iƙirarin cewa na amince da Dr. Hamzat a matsayin ɗan takarar gwamnan jiha na jam’iyyarmu, da kuma goyon bayana ga shawarwarin GAC, tsarin da ban ma sanya hannu a ciki ba."
- Samuel Ajose
'Dan siyasar ya musanta fitar da sanarwar
Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana rubutun a matsayin mai cike da yaudara da ƙeta, sannan ya yi kira ga jama’a da gidajen yaɗa labarai da su yi watsi da sanarwar tare da kauce wa ci gaba da yaɗa ta.
“Wannan rubutu shaci-faɗi ne, ba a ba da izinin fitar da shi ba, kuma an yi shi ne da nufin ƙeta. Ba ya wakiltar matsayina, ko matsayin ƙungiyar yaƙin neman zaɓena, ko matsayin kowane mutum da aka ba wa ikon yin magana a madadina."
“Ina buƙatar mutanen kirki na jihar Legas da magoya bayana a faɗin ƙasar nan da su yi watsi da shi baki ɗaya."
"Bugu da ƙari, ina kira ga gidajen yaɗa labarai masu nagarta da su guji yaɗa abin da ke matsayin ɓatanci da kuma laifi a fannin shari’a, wanda aka tsara shi don yaudarar ra’ayin jama’a da kuma lalata mutuncina."
- Samuel Ajose

Source: Twitter
Wane mataki zai dauka wajen neman takara?
Haka kuma, mai shirn neman takarar gwamnan na APC ya fitar da gargaɗi ga waɗanda ke da hannu wajen yaɗa takardar, inda ya buƙaci su janye ta cikin gaggawa.
“Dukkan ɓangarorin da suka wallafa ko suke ci gaba da yaɗa wannan takarda ana gargadinsu, dole ne a janye ta kuma a goge ta baki ɗaya cikin sa’o’i 12. Idan ba haka ba, za a ɗauki matakin shari’a kan bata suna ba tare da ƙarin wata sanarwa ba."
- Samuel Ajose
Yusuf Buhari ya samu takara karkashin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta cimma matsaya kan batun takarar Yusuf Buhari, dan marigayi Muhammadu Buhari.
Masu ruwa da tsaki na APC sun amince Yusuf Buhari ya fito a matsayin dan takarar jam'iyyar domin wakiltar mazabun Daura/Sandamu/Mai'adua a majalisar wakilai.
Mazabar tarayya da Yusuf Buhari ke son wakilta ta ƙunshi kananan hukumomi uku: Sandamu, Daura, da Mai’adua a jihar Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

