Tsohon Shugaban Ƴan Sanda Ya Ƙi Yarda da Sulhu, Ya Sayi Fom ɗin Takarar Gwamna

Tsohon Shugaban Ƴan Sanda Ya Ƙi Yarda da Sulhu, Ya Sayi Fom ɗin Takarar Gwamna

  • Tsohon sufeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ƙi amincewa da tsarin maslaha wajen zaben d'an takarar gwamna a Nasarawa
  • Adamu, ya sayi fom din neman tsaya wa takara a karkashin jam'iyyar APC, lamarin da ya saba da matsayar Gwamna Abdullahi na nuna magajinsa
  • Ofishin yakin neman zaben Adamu, ya ce tsohon IGP yana da farin jini, zai iya lashe tikitin takara a zaben fitar da gwani kuma ya ci zaben gwamna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Nasarawa – Takaddama ta kunno kai a cikin jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa gabanin zaɓen fitar da gwani na ranar 21 ga watan Mayu, 2026.

Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, ya fito fili ya ƙalubalanci matakin gwamna mai ci na marawa Sanata Ahmed Wadada baya.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sayi fom din takarar gwamnan Nasarawa.
Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya mika fom din takararsa ga Tanko Almakura a Abuja. Hoto: George Udom
Source: Facebook

Tsohon shugaban 'yan sanda zai fito takarar gwamna

Mohammed Abubakar Adamu ya sayi fom din takara a APC, inda ya jaddada cewa ba zai janye takararsa domin wata maslaha ba, in ji rahoton The Punch.

Wannan na kunshe ne a jawabin da Musa Hussein, daraktan yaƙin neman zaɓen Adamu ya yi ga manema labarai a sakatariyar ƙungiyar ƴan jarida (NUJ) da ke Lafia a ranar Talata.

Musa Hussein, ya tabbatar da cewa tsohon IGP ya riga ya sayi fom ɗin nuna sha'awa da na takara, don haka ba shi da wani shiri na janyewa, domin manufarsu ita ce fafatawa a zaɓen fitar da gwani, kowa ya iya allonsa ya wanke.

"Ba za mu amince da sulhu ba saboda mu za mu shiga zaben fitar da gwani ne da yakinin yin nasara, kuma mu lashe babban zaben a 2027.
"A yau, ubangidana, Mohammed Abubakar Adamu, ya sayi fom din nuna sha'awa da kuma na tsaya wa takara a karkashin jam'iyyar APC.”

Kara karanta wannan

Zulum ya yi abin mamaki, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

— Musa Hussein.

Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sayi fom din takarar gwamnan Nasarawa.
Musa Hussein, daraktan yaƙin neman zaɓen tsohon sufetan 'yan sanda ya karbi fom din takararsu a APC. Hoto: George Udom
Source: Facebook

Zargin shishshigin gwamna a fitar da 'yan takara

Da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Abdullahi Sule ya riga ya zaɓi Sanata Ahmed Wadada, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Yamma, a matsayin wanda yake so ya gaje shi.

Sai dai bangaren Mohammed Adamu ya soki wannan mataki, inda suka bayyana shi a matsayin "abin da ya saba wa doka" da tsarin mulki gaba daya, in ji rahoton The Guardian.

Daraktan yaƙin neman zaɓen ya yi gargaɗin cewa tsarin mulkin APC ya yarda da hanyoyi biyu ne kawai na fitar da ɗan takara: kato-bayan-kato da kuma maslaha idan kowa ya yarda.

'Ana son hana ni takara' - Adamu

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban ‘yan sanda, Mohammed Adamu Abubakar, ya zargi shugabannin jam’iyyar kan fitar da dan takara.

Tsohon dan sandan wanda kuma yana daga cikin masu neman takarar gwamnan Nasarawa ya ce ana shirin karkatar da zaɓen fitar da gwani mai zuwa.

Mohammed Adamu ya ce ana matsa wa shugabannin gundumomi a dukkan gundumomi 147 su mara wa ɗan takarar da gwamna ya fi so baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com