Ganduje, Manyan APC Saya wa Abba Fam, An Tara N50m don Takarar Tinubu a 2027
- Jiga-jigan APC a Kano sun saya wa gwamna Abba Kabir Yusuf fam domin ya nemi takara gabanin zaben 2027 mai zuwa
- An kuma amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa domin ya samu damar Zarewa zuwa 2031
- Jam’iyyar ta ce matakin na nufin karfafa hadin kai da tabbatar da nasara a zaben 2027 da a yanzu haka ya tashi yana siyasa tsaye
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jiga-jigan APC a jihar Kano sun saya wa gwamna Abba Kabir Yusuf fam, inda suka ayyana shi a matsayin dan takarar gwamna guda na jam’iyyar a zaben shekarar 2027.
An sanar da wannan mataki ne yayin wani taron jiga-jigan jam’iyyar da aka gudanar a Kano, inda shugabannin jam’iyyar suka tabbatar da cikakken amincewarsu da jagoranci da ayyukan Gwamna Yusuf.

Kara karanta wannan
Mai son takarar gwamna a APC ya ki yarda da zabin Tinubu, ya yi barazanar zuwa kotu

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa hakan na kunshe a cikin wata sanarwar manema labarai da sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Juma’a 1 ga watan Mayu, 2026.
APC ta tsayar da Abba takarar gwamna a 2027
Politics Nigeria ta wallafa cewa da yake mika fam din a madadin jiga-jigan, tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniya ta bai daya da aka cimma domin daukar gwamnan a matsayin dan takarar hadin kai.
Ya ce:
"Mun riga mun amince cewa kai ne dan takarar gwamnanmu, kuma domin cika wannan alkawari, ina mika maka wadannan muhimman fam guda biyu — na nuna sha’awar neman takara da na tsayawa takara — domin ka cike su yadda ya kamata ka kuma gabatar.”aisha

Source: Facebook
Jiga-jigan sun bayyana cewa sayen fam din wata hanya ce ta nuna jajircewarsu wajen tabbatar da hadin kan jam’iyya da kuma ci gaba da dorewar nasarorin da aka samu a karkashin wannan gwamnati.
Sun kara da cewa tsarin dan takara guda zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da sahihin tafiyar zabe a 2027.
2027: An goyi bayan Tinubu a Kano
A nasa bangaren, gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode da wannan karamci, inda ya sake jaddada kudirinsa na tafiyar da mulki mai hada kowa da kowa, aiwatar da manufofin da suka shafi talakawa, da kuma ci gaba da bunkasa jihar Kano.
A wani bangare kuma, jiga-jigan APC a Kano sun kuma amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa guda na jam’iyyar a zaben 2027, tare da alkawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 50 domin sayen fam dinsa.
An cimma wannan matsaya ne a wani babban taro da aka gudanar a dakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin Kano.
Rabiu Sulaiman Bichi ne ya gabatar da kudirin amincewar, wanda dukkannin mahalarta taron suka mara masa baya baki daya.
Shugaban APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa da farko jam’iyyar ta yi tunanin sayen fam din kai tsaye, amma daga bisani ta amince da bayar da gudummawar kudi.
Ya ce:
"Mun amince mu bayar da Naira miliyan 50 domin sayen fam din nuna sha’awa da na tsayawa takara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Jiga-jigan sun ce sun dauki wannan mataki ne bisa amincewa da jagorancin shugaban kasa da sauye-sauyen da yake aiwatarwa, tare da kudurin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2027.
Abba ya magantu kan zaben mataimakin gwamnan Kano
A wani labarin kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kare matakin da ya dauka na nada Hon. Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da nadin da aka yi wa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Murtala Sule Garo ya cancanci mukamin da aka ba shi domin mutum ne da zai iya ba da gudunmawar da ta dace.
Asali: Legit.ng

