Trump Ya Yi Magana kan Dan Amurka da aka Sace a Nijar
- Donald Trump ya tabbatar da an Ba’amurke mai wa’azi, Kevin Rideout, wanda ya shafe sama da watanni tara a hannun masu garkuwa da mutane a Nijar
- Shugaba Trump ya ce Rideout ya sake haduwa da matarsa, Krista, kuma yanzu yana shirin komawa Amurka bayan samun ‘yancinsa
- Shugaban Amurkan ya bayyana hakane a ranar Lahadi, inda ya ce Rideout na daga cikin ‘yan Amurkan da aka kubutar tun bayan da ya fara wa’adinsa na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa an saki wani Ba’amurke mai wa’azi, Kevin Rideout, bayan shafe sama da watanni tara a tsare a Nijar.
Trump ya ce Rideout ya sake haduwa da matarsa, Krista, kuma yana shirin tashi zuwa Amurka.

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa Trump ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 'yan kwanaki bayan ceto mutumin daga hannun masu garkuwa da mutane.
Trump ya rubuta cewa:
“Na yi farin cikin bayyana cewa tsohon wanda aka yi garkuwa da shi, Kevin Rideout, yana shirin komawa Amurka bayan ya sake haduwa da kyakkyawar matarsa, Krista.”
Ya ce sakin Rideout ya zama “Ba’amurke na 110 da aka kubutar daga zaman fursuna” tun bayan da ya fara wa’adinsa na biyu a matsayin shugaban Amurka.
Shugaba Donald Trump ya kara da cewa yana fatan ganin Rideout da matarsa a Fadar White House nan ba da jimawa ba.
Yadda aka sace shi a Nijar
Rideout, wanda Kirista ne mai wa’azi kuma matukin jirgi na kungiyar SIM International, ya shafe sama da watanni tara a hannun masu garkuwa da mutane bayan da aka sace shi a wajen gidansa da ke Yamai, babban birnin Nijar a 2025.
BBC ta wallafa cewa kungiyar SIM International ta ce Rideout na cikin koshin lafiya kuma jami’an Amurka ne ke kula da shi bayan an sake shi.
Rahotanni sun ce wasu mutane uku dauke da makamai ne suka yi garkuwa da mai wa’azin, inda suka tafi da shi zuwa yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar, wani yanki da ke fama da hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai.

Source: Getty Images
Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka samu sakin Rideout ba, ciki har da wadanda suka yi garkuwa da shi da kuma yadda aka cimma yarjejeniyar sakin nasa.
Rideout ya shafe shekaru 19 yana aiki a Nijar, inda ya kasance matukin jirgi na SIM International, wata kungiyar Kirista da ke gudanar da ayyuka a kasashe sama da 70.
Batun jefa nukiliya Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohuwar ‘yar majalisar wakilan Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta yi ikirarin cewa gwamnatin Donald Trump na gudanar da taruka kan yiwuwar amfani da nukiliya a Iran.
Greene, wadda a baya ta nuna adawa da shigar Amurka cikin yakin Iran, ta ce an tattauna batun amfani da makaman nukiliya a kan Iran a wasu manyan tarukan gwamnati.
Sai dai tsohuwar ‘yar majalisar ba ta gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da ikirarin nata ba, kuma har yanzu ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka ba.
Asali: Legit.ng

