Atiku Ya Ce Zubar da Jinin 'Yan Najeriya zai Kawo Karshen Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi wa shugaban kasa Bola Tinubu raddi kan cewa ba zai fadi zaben 2027 ba
- Bola Tinubu ya sanar da cewa wasu mutane na son amfani da rashin tsaro wajen hana shi nasara a zaben 2027 amma ba zai yarda ba
- A martanin da Atiku Abubakar ya yi, ya bayyana cewa zubar da jinin da ake a Najeriya zai kawo karshen mulkin shugaban kasar a 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fusata kan kalaman da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi cewa matsalar rashin tsaro ba za ta sa ya fadi a mulki ba.
Atiku Abubakar ya yi martani yana mai cewa irin wannan magana na nuna rashin fahimtar halin kunci da miliyoyin ‘yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan
"Zan fito kamfe," Tinubu ya gano abin da 'makiyansa' ke shirin yakarsa da shi a zaben 2027

Source: Facebook
Raddin Atiku ga Bola Tinubu
Daily Trust ta wallafa cewa Atiku ya ce shugabanci ba ya dorewa da taurin kai, sai dai da yin adalaci, tausayi, da kuma daukar matakan da ake gani suna iya magance matsalolin kasa.
Sai dai ya jaddada cewa a bayyane yake gwamnati ta gaza matuka wajen babban aikinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
“Ba ‘yan adawa ba ne za su yi hukunci kan wannan gwamnati — jininnin bayin Allah da ake zubarwa a kullum shi ne zai yi magana. Wannan jini zai yi tasiri fiye da kowace irin magana ta siyasa,”
In ji shi.
Maganar Atiku kan zubar da jini
Atiku Abubakar ya koka cewa yawan zubar da jini a karkashin gwamnatin Bola Tinubu ya kai matakin da ba za a iya lamunta ba.
Ya ce sama da ‘yan Najeriya 10,000 aka kashe tun daga watan Mayu 2023, yayin da wani kiyasi ke nuna cewa sama da 18,000 aka rasa cikin shekaru biyu sakamakon rashin tsaro.

Source: Facebook
Maganar kifar da Tinubu
Atiku ya ce ba wanda ke kokarin tilasta Shugaban kasa ya sauka daga mulki illa raguwar amincewar jama’a sakamakon yadda gwamnati ke tafiyar da al’amura ne.
The Cable ta rahoto ya ce tsadar rayuwa, manufofin tattalin arziki marasa tsari, da kuma karuwar rashin tsaro su ne ke sa ‘yan Najeriya ke rasa amincewa da Tinubu.
“Dole ne shugabanci ya samu amincewa daga jama’a, ba a tilasta shi,”
In ji shi.
Ya kuma gargadi cewa yunkurin tsoratar da ‘yan adawa ba zai ceto gwamnatin da ta gaza ba:
“Babu wata hanya da za ta iya boye gaskiyar halin da ‘yan Najeriya ke ciki. A karshe, jama’a su ne za su yanke hukunci bisa abin da suka gani a kasa.”
Shettima ya gargadi 'yan APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya gargadi 'yan APC kan zaben 2027.
Shettima ya bukaci dukkan masu neman takara da su tsaya a jam'iyyar ko da sun fadi zaben fitar da gwani da APC ke shirin farawa.
Ya bayyana cewa dole ne wasu su fadi a zaben fitar da gwani kasancewar tsarin ya nuna cewa mutum daya ne zai samu tikitin takara.
Asali: Legit.ng

