"Ba Aibu ba ne," Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Bashi da Yake Ciyo wa Najeriya

"Ba Aibu ba ne," Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Bashi da Yake Ciyo wa Najeriya

  • Shugaba Bola Abmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai daina karbo wa Najeriya bashin kudi ba matukar akwai bukatar hakan
  • Tinubu ya ce maimakon sukar ciyo bashin da ake yi, kamata ya yi Najeriya ta dage wajen ganin ta biya basussukan da ke kanta
  • Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da karbo rancen kudi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karbar bashi idan bukatar hakan ta taso, yana mai cewa bai kamata a dauki hakan a matsayin aibu ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Aso Rock yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar Plateau karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang da Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zubar da jinin 'yan Najeriya zai kawo karshen Tinubu a 2027

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na jawabi a wurin taro a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A rahoton The Cable, shugaban kasar ya ce karbo aron kudi ba aibu ba ne kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da karbowa idan akwai bukatar hakan.

“Idan ta kama dole mu karbo bashi, za mu karba, cin bashi ba aibu ba ne, abin da ya ya kamata shi ne mu yi aiki tukuru domin mu iya biyansa," in ji shi.

Yadda Bola Tinubu yake ta karbo bashi

Wannan bayani na zuwa ne a lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda bashin Najeriya ke karuwa da kuma yadda ake kashe kaso mai yawa na kudaden shiga wajen biyan bashin.

A ranar Talatar nan, Majalisar wakilai ta amince da bukatar shugaban kasa ta sake karbo bashin Dala miliyan 516.3 domin gina wasu sassan hanyar Sokoto zuwa Badagry.

Haka kuma a ranar 31 ga Maris, 2026, Tinubu ya nemi amincewar majalisa kan karbar bashin waje da ya kai Dala biliyan 6.

Kara karanta wannan

"Zan fito kamfe," Tinubu ya gano abin da 'makiyansa' ke shirin yakarsa da shi a zaben 2027

Bashin nawa ake bin Najeriya a yau?

Bashin da ake bin Najeriya ya kunshi na cikin gida da na waje na gwamnatin tarayya da kuma na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (Abuja).

A ranar 15 ga Afrilu, Hukumar Kula da Basussuka (DMO) ta bayyana cewa jimillar bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.27 a karshen zangon karshe na shekarar 2025.

Gwamnatin tarayya ce ke da kaso mafi tsoka, inda bashin cikin gida ya kai N80.48tn, yayin da bashin waje ya kai Dala biliyan 51.85.

Haka zalika gwamnatocin jihohi da na babban birnin Abuja kuma na da bashin N8.15tn a kan su a yau.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin wani taro a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: UGC

Tun a watan Maris na 2024, DMO ta bayyana cewa bashin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 97.34 a karshen 2023, sakamakon sabbin basussukan cikin gida da gwamnatin tarayya ta karba domin cike gibin kasafin kudin 2024.

Duk da haka, Tinubu ya tabbatar wa yan Najeirya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karbo rance idan bukatar hakan ta taso, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abba ya gano yan siyasar da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya

Tinubu ya samu damar ciyo bashi

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dattawa ta sahalewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbo bashin Dala miliyan 516 domin gina titin Sokoto zuwa Badagry.

Amincewar ta biyo bayan nazari da Majalisar dattawan ta yi kan rahoton da kwamitin kula da basussukan cikin gida da na waje ya gabatar a zaman jiya Laraba.

Rahoton ya nuna cewa bashin yana da garantin kariya daga Hukumar Musulunci ta Inshorar Zuba Jari da Bayar da Lamuni (ICIEC), kuma za a biya shi cikin shekaru tara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262