Sanata Ya Daina Jayayya, Ya Bi bayan Dan Takarar Gwamna da Zulum Ya Tsayar a Borno
- Sanata Kaka Shehu Lawan ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamna da Babagana Umara Zulum ya tsayar a Borno
- 'Dan majalisar dattawan wanda ke wakiltar Borno ta Tsakiya ya fara bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamna a jihar gabanin 2027
- Sai dai Gwamna Babagana Umara Zulum ya riga ya tsayar da Mustapha Gubio a matsayin wanda APC ta sa wa albarka ya tsaya takara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Sanatan da ke wakiltar Borno ta Tsakiya, Kaka Shehu Lawan, ya janye daga takarar gwamnan jihar, inda ya bayyana goyon bayansa ga babban abokin takararsa, Mustapha Gubiom.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna Hon Mustapha Gubiom a matsayin wanda yake so ya gaje shi bayan zaben 2027.

Kara karanta wannan
Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mataimakin sanatan a majalisa, Usman Alkali, ya fitar a ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, 2026, ya tabbatar da janye takarar mai gidansa.
An cimma matsaya kan takarar gwamnan Borno
Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa an cimma wannan matsaya ne bayan wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar sanarwar da Usman Alkali ya fitar, ya ce an roki Kaka Shehu Lawan ya janye domin bai wa Gubio dama ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar a 2027.
Sanarwar ta ce:
“A taron masu ruwa da tsaki da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta a daren Alhamis, wanda ya samu halartar Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa, Ali Bukar Dalori; Ministan Noma, Abubakar Kyari; ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa; da kuma Ƙungiyar Dattawan Borno, an yanke shawarar roƙon Sanata Kaka Shehu Lawan da ya janye daga takarar gwamna domin bai wa Injiniya Mustapha Gubio damar zama ɗan takarar APC a Borno.”
Ya ƙara da cewa, bisa wannan matsaya, ana sa ran sanatan zai ci gaba da riƙe kujerarsa a Majalisar Dattawa domin wakiltar Borno ta Tsakiya.
Dalilan da suka jawo cimma matsaya a Borno
Alkali ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa dimokuraɗiyya, tabbatar da haɗin kai, da kuma samar da daidaito a cikin jam’iyyar APC a jihar Borno.
Ya ce:
“Haka zalika, Sanata Kaka Shehu Lawan zai ci gaba da riƙe kujerarsa a matsayin sanatan da ke wakiltar Borno ta Tsakiya.”

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa, karkashin jagorancin Gwamna Zulum, ana sa ran ‘yan takara da sauran jiga-jigan siyasa za su isa jihar a ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, 2026 inda dubunnaan magoya baya za su tarbe su a Maiduguri.
A wani ɓangaren kuma, mai magana da yawun gwamnan jihar, Dauda Illiya, ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Borno ta amince da Mustapha Gubio a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya.
Ya ce Gwamna Zulum ya gabatar da Gubio ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Mai son takarar gwamna a APC ya ki yarda da zabin Tinubu, ya yi barazanar zuwa kotu
'Dan majalisa ya hakura da takara a Borno
A baya, mun wallafa cewa mataimakin kakakin majalisar dokokin Borno, Abdullahi Musa Askira ya janye daga takarar Sanatan Kudancin yankin.
Ya bayyana cewa ya hakura ne bayan jam'iyya mai mulki ta APC ta amince ta sake mara wa Sanata Ali Ndume baya don ya sake neman kujerar da ya ke kai a 2027.
Abdullahi Musa Askira ya kuma aika sako ga magoya bayansa daga yankin Borno ta Kudu, inda ya ce mulki daga Allah ne, kuma zai ci gaba da mara wa Ndume baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
