Sanata Ya Yi wa Gwamna Kara, Zai Ajiye Kujerarsa a Majalisa domin ba Shi Wuri
- Sanatan Yobe ta Gabas, Mustapha Musa, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a 2027
- Mustapha Musa ya janye daga takarar 2027 tare da marawa Gwamna Buni baya a matsayin magajinsa a zaben shekarar 2027
- Sanatan ya bayyana cewa ya amince da matsayar shugabannin jam’iyya, tare da umartar magoya bayansa su yi biyayya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Sanatan Yobe ta Gabas, Mustapha Musa, ya sanar da janyewarsa daga takarar zaɓen 2027 da ke tafe.
Sanata Musa ya dauki wannan mataki ne domin ba Gwamna Mai Mala Buni dama tare da bayyana goyon bayansa domin ya nemi kujerar.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook, sanatan ya ce ya yanke shawarar ne domin biyayya ga matsayar shugabannin jam’iyyar APC da tsarin siyasar da aka tsara.

Kara karanta wannan
Masarautar Ilorin ta gano amfanin Tinubu a ofis, ta goyi bayan ya zarce zuwa 2031
Sanata ya janye takara ga Gwamna Buni
Mustapha Musa, wanda aka fi sani da Kulas, ya ce ba zai nemi wata kujera ta siyasa ba bayan janyewarsa daga fafatawar neman tikitin takara.
Sanatan ya kuma umarci magoya bayansa da su daina yaɗa takardu da sauran kayan kamfen da ke nuna shi a matsayin ɗan takarar wata kujera.
Ya ce:
“Na sanar da janyewa ta a hukumance daga fafatawar neman tikitin takarar, shi, ba zan nemi wata kujerar zaɓe ba."
Hakazalika, ya taya tsohon Sakataren Gwamnatin Yobe, Baba Mallam Wali, murnar zama wanda shugabannin jam’iyya suka zaɓa domin takarar gwamna.
Ya yi wa Wali da sauran ’yan takarar APC fatan samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Source: Facebook
Godiya marar adadi daga sanatan ga Buni
Sanatan ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Mai Mala Buni da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Ibrahim Geidam, bisa goyon baya da shawarwarin da suka ba shi tsawon rayuwarsa ta siyasa.

Kara karanta wannan
"Mulki na Allah ne": Mataimakin shugaban majalisa ya hakura da neman kujerar sanata Ndume
Ya ce taimakon nasu ne ya taimaka masa tun daga lokacin da yake Sakataren Hukumar Tallafin Karatu ta Yobe har zuwa kwamishina da kuma zama sanata.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Kulas surukin Ibrahim Geidam ne wanda ministan ya auri ’yarsa ta cikinsa.
Haka kuma, Gwamna Mai Mala Buni ma surukin Geidam ne, ya auri ’yarsa jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a 2019.
Wasu magoya bayan siyasa sun bayyana cewa matakan da ake ɗauka a siyasar Yobe na nuna ƙoƙarin APC wajen ƙarfafa haɗin kai da haɗa kowa gabanin zaɓen 2027.
APC, Mala Buni sun fitar da magajin gwamna
A wani labarin, an ji cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Yobe sun bayyana wanda suke so ya tsaya masu takarar gwamna a zaben 2027 da ke tafe.
Rahotanni sun nuna cewa sun bayyana matsayarsu ne yayin wani zama da suka yi a birnin tarayya Abuja tare da gwamna Mai Mala Buni.
Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana dalilan zaben Baba Malam Wali a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar APC takara a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng