Masarautar Ilorin Ta Gano Amfanin Tinubu a Ofis, Ta Goyi bayan Ya Zarce zuwa 2031

Masarautar Ilorin Ta Gano Amfanin Tinubu a Ofis, Ta Goyi bayan Ya Zarce zuwa 2031

  • Majalisar masarautar Ilorin da ke jihar Kwara ta bayyana cewa akwai buƙatar shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa’adi na biyu
  • Haka kuma ta bayyana Sanata Saliu Mustapha a matsayin ɗan takarar gwamna da aka fi so a 2027 domin ciyar da yankin gaba
  • Majalisar ta ce goyon bayan da ta nuna tun yanzu ba yana nufin an hana sauran ‘yan takara fafutukar neman kujerun ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara – Majalisar ba da shawara ta masarautar Ilorin (IEPAC) ta bayyana goyon bayanta ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara karo na biyu a 2027.

Haka kuma, majalisar ta ayyana Sanata Saliu Mustapha a matsayin ɗan takarar gwamna da ta fi so domin a ciyar da jihar Kwara gaba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karyata jita jita, ya jero ayyukan da gwamnatinsa ke yi a yankin Arewa

An nemi Tinubu ya sake wa'adi na biyu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Yan majalisar masarautar Ilorin yayin amincewa da shugabancin Tinubu Hoto: Tinubu Reporters/Facttimes
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a sanar da wannan matsaya ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Bola Tinubu ya samu goyon baya a Ilorin

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yayin taron, shugabannin majalisar sun bayyana alkiblar siyasar masarautar gabanin babban zaɓen ƙasa mai zuwa.

IEPAC dai ita ce babbar ƙungiya ta dattawa da masu ruwa da tsaki a yankin Sanatan Kwara ta Tsakiya kuma tana fada a ji a siyasa.

A cewar majalisar, sun ɗauki wannan matsaya ne bayan nazari mai zurfi da kuma tantance ‘yan takara da ke neman manyan muƙamai daga na shugaban ƙasa har zuwa na majalisar dokoki ta ƙasa.

Yadda aka amince da Tinubu a Masarautar Ilorin

Da yake jawabi ga manema labarai, mai kula da ayyukan majalisar a ƙasa, Dakta Yakub Yahaya Oloriegbe, tare da sakataren majalisar, Laftanar Kanal Abubakar Edun, sun ce an yi duba na tsanaki kan masu neman muƙamai daban-daban.

Kara karanta wannan

An rarrashi yar tsohon shugaban kasa da aka buge ta a neman takarar gwamna

Oloriegbe ya ce majalisar ta yi la’akari da ayyukan da Tinubu ya gudanar cikin shekaru uku da suka gabata, musamman irin dama da goyon bayan da aka bai wa yankin Kwara ta Tsakiya a wannan lokaci.

Ya ce:

“Mun amince baki ɗaya da goyon bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin wa’adi na biyu."
An nemi Sanata Sabiu Mustapha ya nemi takarar gwamna a Kwara
Wasu daga cikin ƴan majalisar masarautar Kwara a wurin taron goyon bayan Tinubu Hoto: Facttimes
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa majalisar na ganin shugaban ƙasar ya cancanci karin shekaru huɗu domin ya ƙarfafa nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu.

Game da takarar gwamna kuwa, majalisar ta bayyana Sanata Saliu Mustapha a matsayin wanda ya dace da jagoranci, tana mai cewa yana da karɓuwa sosai a tsakanin al’umma kuma yana da ƙwarewar da za ta iya taimaka wa jihar Kwara.

A cewar majalisar, zaɓin Mustapha ya samo asali ne daga fahimtar cewa yana da gogewa da kuma kusanci da jama’a, wanda hakan zai taimaka wajen inganta shugabanci a jihar idan aka ba shi dama.

Sai dai majalisar ta yi ƙarin haske cewa wannan goyon baya ba yana nufin hana sauran ‘yan takara shiga takara ba ne.

Shugaba Tinubu ya magantu kan ayyukansa

A baya, mun wallafa cewa fadar shugaban Ƙasa ta musanta zargin cewa an yi watsi da yankin Arewa maso Yamma, ta ce ana gudanar da manyan ayyuka a shiyyar.

Kara karanta wannan

Tsohon sufeta janar ya zargi APC da neman hana shi takarar gwamna

Gwamnati ta bayyana haka ne yayin da ake zargin ta yi watsi da yankin Arewa maso Yamma yayin da ta nuna fifiko wajen ayyukan raya wasu sassan Najeriya.

Ta bayyana cewa daga cikin manyan ayyukan a yankin akwai aikin layin dogo na Kano–Maradi mai darajar $2bn, wanda aka kai kusan 60% na kammala shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng