Rurum Ya Samu Goyon baya domin Maye Gurbin Kawu Sumaila a Majalisar Dattawa

Rurum Ya Samu Goyon baya domin Maye Gurbin Kawu Sumaila a Majalisar Dattawa

  • Shugabannin kananan hukumomi 16 a Kano ta Kudu sun marawa Kabiru Rurum baya takarar Sanata a yankin
  • Sun ce matakin ya biyo bayan tuntuba da shugabanni da ‘yan majalisa a yankin yayin da ake shirin tunkarar 2027
  • Shugabannin sun ce goyon bayan na da nufin kare APC daga faduwa warwas da mika kujerar ga ‘yan adawa a badi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugabannin kananan hukumomi 16 daga yankin Kano ta Kudu sun bayyana goyon bayansu ga Hon. Kabiru Alhassan Rurum a matsayin wanda suke so ya wakilce su a kujerar Sanata karkashin jam’iyyar APC a zaben 2027.

A wata sanarwa da suka fitar bayan sun yi zama da shawarwari da majalisun kananan hukumominsu, shugabannin jam’iyya da kuma ‘yan majalisu a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Ana goyon bayan Rurum a Kano ta Kudu
Dan majalisar wakilai, Kabiru Alhassan Rurum daga jihar Kano. Hoto: Fatihu Yusuf Abdullahi
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugabannin sun ce sun dauki wannan mataki ne domin mara wa Rurum baya a fafatawar da ake sa ran zai yi da Sanata mai ci, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila.

Kano: 'Yan APC sun goyi bayan Kabiru Rurum

21st century chronicle ta wallafa cewa sanarwar ta ce an cimma matsayar ne baki daya, inda aka jaddada bukatar ci gaba da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ‘yan jam’iyyar APC a yankin.

Haka kuma, shugabannin sun ce wannan goyon baya na nufin kara karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar, tare da tabbatar da ingantacciyar wakilci ga al’ummar Kano ta Kudu a matakin kasa.

Kabiru Rurum, wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure a Majalisar wakilai, na daya daga cikin manyan ‘yan siyasa da ake ganin suna da tasiri a yankin.

Dalilin goyon bayan Hon. Rurum a Kano

Da yake tabbatar da wannan ci gaba, Mataimakin shugaban karamar hukumar Bebeji, Ali Sarkin Yaki, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kare muradun jam’iyyar APC a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

2027: Ana rade radin za a sauya shi, matasa sun tara wa Sanata Ndume kudin fam sama da N38m

A cewarsa:

“Mun dauki wannan shawara ne domin ceto jam’iyya a zaben 2027, saboda muna ganin hakan zai taimaka wajen hana yankin fadawa hannun ‘yan adawa.”
Ana son dawo da Masu Sumaila daga kujerarsa
Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila Hoto: @KawuGarba
Source: Twitter

Ya kara da cewa hadin kai da goyon bayan da suka nuna zai taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a yankin Kano ta Kudu.

Sai dai, wani na kusa da Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce sun san da wannan matsaya, amma sun ki yin karin bayani a kai a halin yanzu.

A cewarsa:

“Mun gani, amma ba yanzu ba ne lokacin yin magana a kai. Za mu mayar da martani kan dukkannin batutuwan da aka taso da su a lokacin da ya dace.”

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke kara daukar zafi gabanin zaben shekarar 2027, inda ake ganin yankin Kano ta Kudu zai kasance daya daga cikin wuraren da za a fafata sosai tsakanin manyan ‘yan siyasa da jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House

Kabiru Rurum ya koma APC a Kano

A baya, mun wallafa cewa siyasar jihar Kano ta sake rikicewa bayan Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai daga NNPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Rurum wanda ke wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure ya taba rike mukamin kakakin majalisar Kano, kuma dama tsohon mamba ne na jam'iyya mai mulki ta APC .

Ra'ayoyin jama'a sun rabu a kan sauya shekar; wasu sun zarge shi da son kai, yayin da wasu ke ganin hakan wani tasiri ne na siyasar 2027 da ke tafe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng