Shugaba Tinubu Ya Zabi Wanda Yake So Ya Gaji Kujerar Gwamnan Legas a Zaben 2027
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya goyi bayan zabin Majalisar GAC ta jihar Legas game da wanda zai yi wa APC takarar gwamna a 2027
- Tinubu ya amince da zabin mataimakin gwamna, Dr. Obafemi Hamzat a matsayin wanda zai gaji kujerar gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu
- Wannan amincewa ta Tinubu ta biyo bayan jerin goyon bayan da Hamzat ya samu a cikin jihar, ciki har da na Gwamna Babajide Sanwo-Olu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana zabinsa game da 'yan takarar da ke neman kujerar gwamnan jihar Legas karkashin inuwar APC a zaben 2027.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ayyana goyon bayansa ga mataimakin gwamna, Dr. Obafemi Hamzat a matsayin wanda yake son ya zama magajinsa.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta ba Tinubu damar ciyo bashin Dala miliyan 516 daga kasar waje

Source: Twitter
Bola Tinubu ya goyi bayan Obafemi Hamzat
Tashar TVC News ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya amince tare da goyon bayan Hamzat a matsayin 'dan takarar gwamnan APC a zaben gwamnan Legas na shekarar 2027.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Majalisar dattawan APC mai ba da Shawara kan Harkokin Mulkin jihar Legas (GAC) a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
GAC ta gabatar da Hamzat ga Tinubu
Majalisar ta GAC, karkashin jagorancin shugabanta, Tajudeen Olusi, ita ce ta gabatar da Hamzat ga Shugaba Tinubu.
Yayin wannan ziyara, Olusi ya bayyana matakin zaben Obafemi Hamzat a matsayin yarjejeniya da dattawan jam’iyyar APC na jihar Legas suka amince da ita baki daya.
Wannan amincewa ta biyo bayan jerin goyon bayan da Hamzat ya samu a cikin jihar, ciki har da na Gwamna Babajide Sanwo-Olu da kuma amincewar mambobi 34 na majalisar GAC.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya dauko batun nada Murtala Garo mataimakinsa, ya fadi dalilin ba shi mukami
APC za ta shirya zaben fitar da gwani
Duk da cewa wasu masu neman takarar gwamna a inuwar APC sun nuna rashin amincewarsu, majalisar ta GAC ta nace cewa tsarin ya kunshi kowa da kowa.
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa za a gudanar da zaben fitar da gwani kamar yadda ka’idojin jam’iyyar suka tanada domin bai kowa dama ba tare da tauye hakki ba.

Source: Twitter
APC dai ta tsara gudanar da zabukan fitar gwani na yan takarar gwamna a ranar 21 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sai dai ana ganin goyon Shugaba Tinubu, Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Majalisar dattawan Legas za su ba mataimakin gwamnan damar samun tikitin APC fiye da sauran yan takara.
Gwamnan Legas na shirin yin murabus?
A baya, kun ji cewa Gwamnatin jihar Legas ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi murabus saboda dalilan rashin lafiya.
Gwamnatin ta soki wani rahoto da wata kafar yanar gizo ta wallafa cewa gwamnan zai yi murabus, tana mai jaddada cewa babu wani tushe na gaskiya a cikinsa.
Mai ba gwamna Sanwo-Olu shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Gboyega Akosile, ya ce maganar rashin lafiyar ba ta da tushe.
Asali: Legit.ng