"Zan Fito Kamfe," Tinubu Ya Gano Abin da 'Makiyansa' ke Shirin Yakarsa da Shi a Zaben 2027

"Zan Fito Kamfe," Tinubu Ya Gano Abin da 'Makiyansa' ke Shirin Yakarsa da Shi a Zaben 2027

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen neman tazarce kan mulki a zaben 2027
  • Tinubu ya bayyana cewa makiyansa na kokarin amfani da matsalar tsaro wajen kai shi kasa, amma shi dan siyasa ne mai taurin kai
  • Shugaban kasar ya bukaci masu ruwa da tsaki na jihar Filato su sanar da gwamnati duk wanda suka san yana rura wutar rikici a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kansa a matsayin "rigimammen dan siyasa mai taurin kai," wanda makiyansa ke kokarin kayar da shi.

Shugaba Tinubu ya yi zargin cewa makiyansa na kokarin amfani da matsalar tsaron Najeriya domin ganin ya fadi zaben 2027 mai zuwa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da masu ruwa da tsaki na jihar Filato lokacin da suka kai masa ziyara a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Tinubu ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki daga Jihar Filato karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kasar Jamus ta shigo Najeriya, ta shiga kauyukan da aka kai hare hare

Bola Tinubu ya hango shirin makiyansa

Shugaban Najeriyan ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba duk kuwa da sukar da yake sha daga yan adawa kan yanayin tsaro a kasar nan.

Shugaban ya bayyana cewa:

"Kuna buga gangar da take yi wa wakilan barna dadi ne, ciki har da makiyana, wadanda suke son yin amfani da rashin tsaro don su kawar da ni daga mulki.
"Amma ni 'dan siyasa ne rigimamme kuma mai taurin kai matuka. Na ki saduda sam kuma zan yi yakin neman zaben wa'adina na biyu."

Gwamnatin tarayya ta shirya daukar mataki

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki da zaran an gano wadanda ke tunzura jama'a ko kuma masu daukar nauyin tashe-tashen hankula.

"Idan kun gano kuma kun san sunayen masu haddasa fitina, ko wakilan barna, ko masu tunzura mutane wadanda suke son a ci gaba da zubar da jini, to ku sanar da mu. Za mu yi amfani da karfin ofishinmu don mu yi maganinsu," in ji Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abba ya gano yan siyasar da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya

Ya jaddada cewa jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kama irin wadannan mutane da zaran an samu bayanan sirri masu inganci, yana mai cewa dole ne a kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar Filato.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Tinubu yana rattaba hannu kan wani kudiri a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya ja kunnen manyan Filato

Haka zalika, Tinubu ya amince da sabon kwamitin zaman lafiya da aka kafa wanda ya kunshi tsofaffin gwamnonin Jihar Filato, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya umarce su da su yi aiki a matsayin kungiya daya don nazarin duk wasu rahotanni na rikice-rikicen baya da kuma gabatar da shawarwari cikin hadin kai domin daukar mataki.

Shugaban ya ba su shawarar su kira juna su tattauna ba tare da nuna bambanci ba, sannan su duba tsofaffin rahotannin abubuwna da suka faru don cimma matsayar yadda za a aiwatar da su.

Shugaba Tinubu ya yi sababbin nade-nade

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasika ga majalisar dattawa domin neman amincewarta kan nade-naden da ya yi.

Wasiƙar Shugaba Tinubu tana neman tantancewa da kuma tabbatar da mutane 15 da aka zaɓa domin shiga hukumar kare haƙƙin dan adam ta kasa (NHRC).

Shugaban ƙasar ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗe ne bisa ga tanadin sashe na 2(3) na dokar kafa hukumar kare haƙƙin dan Adam ta kasa (2010).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262