'Ba Za Su Yi Nasara ba': Babban Malami Ya Hango abin da Zai Faru da Tinubu a 2027

'Ba Za Su Yi Nasara ba': Babban Malami Ya Hango abin da Zai Faru da Tinubu a 2027

  • Fitaccen fasto, Samuel Ojo, ya ce yunkurin ‘yan adawa na hana Shugaba Bola Tinubu yin tazarce a zaben 2027 ba zai yi nasara ba
  • A cewarsa, Ubangiji ya riga da ya rubuta nasarar Tinubu a 2027, don haka, ko ana ha maza ha mata, Tinubu ne mai nasara a zaben
  • Ojo ya yi gargaɗi ga 'yan adawa da su hakura da 2027, domin Ubangiji bai gama amfani da Tinubu ba, akwai sauran aiki a gabansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Fitaccen fasto mai hasashen siyasa a matakin ƙasa da ƙasa kuma jagoran cocin FARIM, Samuel Adebayo Ojo ya yi hasashe kan zaben 2027.

Prophet Samuel Ojo ya bayyana cewa kawance ko ƙoƙarin ‘yan adawa na hana shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wa’adi na biyu a 2027 ba zai yi nasara ba.

Malamin addini ya hango nasarar Tinubu a 2027 duk da shirye-shiryen kawancen 'yan adawa
Shugaba Bola Tinubu | Tsohon dan takarar PDP, Atiku Abubakar. Hoto: @officialABAT, @atiku
Asali: Facebook

'Yan adawa ba za su hana nasarar Tinubu ba

A cewar Prophet Ojo, komawar Tinubu Aso Rock karo na biyu wata ƙaddara ce ta Ubangiji da dabarun dan Adam ba zai hana ta faruwa ba, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Prophet Ojo ya bayyana wannan hasashen a yayin da yake jagorantar sabuwar ibadar mako-mako ta "Daren sirruka (Oru Asiri)" a hedikwatar cocinsa da ke Ibadan.

A gaban dubban mabiyansa, ya ce kokarin ‘yan adawa na neman kafa babban kawance don kwace mulki daga Tinubu ba zai yi nasara ba domin Ubangiji ya riga ya rubuta nasarar Tinubu a zaben 2027.

A cewar malamin Kiristan:

“Ko 'yan adawa na ha maza ha mata, Tinubu ne zai yi nasara a 2027 don an riga an rubuta cewa zai sake mulki a karo na biyu."

"Ubangiji bai gama aiki da Tinubu ba' - Fasto

Fitaccen malamin addinin da aka sani da hasashen siyasa a lokutan zaɓe ya ja kunnen shugabannin siyasa da ke kokarin tunzura jama’a da gurgunta Tinubu da su daina hakan.

Ya ce makomar Najeriya da kwanciyar hankalinta na da nasaba da tsare-tsaren Ubangiji da ke sa hannu a lamuran wannan gwamnatin, a cewar rahoton Pulse.

“Wadanda ke shirin cire shi ta hanyar dabara, sharri ko haɗin kai, za su tarwatse. Ubangiji bai gama amfani da shi ba. Har yanzu akwai aikin da zai kammala wa ƙasa."

- Prophet Ojo.

Masana na ganin 'yan adawa za su gamu da kalubule a 2027 a kokarinsu na kifar da Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

'Yan adawa za su gamu da kalubale a 2027

Wannan hasashe ya fito ne a daidai lokacin da siyasar Najeriya ke ɗaukar sabon salo, inda ake ganin wasu fitattun jiga-jigan adawa na shirin kafa kawance domin tunkarar zaben 2027.

Duk da sukar gwamnatin Tinubu kan tabarbarewar tattalin arziki da tsaro, magoya bayansa na jaddada cewa yana buƙatar ƙarin lokaci don aiwatar da sauye-sauyen dogon lokaci.

Yayin da hasashen Prophet Ojo ya jawo cece-kuce, mabiyansa na ganin hakan matsayin tabbaci daga Ubangiji. Sai dai ‘yan adawa na kallon hakan a matsayin kirkirarren zance kawai.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa sun gamu cewa yawancin hasashen Sam Ojo na tabbata, don haka zaben 2027 na iya kasancewa ƙalubale ga masu adawa da Tinubu fiye da yadda ake zato.

El-Rufai, Atiku sun hango nasara a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai sun hango nasara a zaben 2027.

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kakaba wa 'yan Najeriya talauci da gangan domin kawai ya ci gaa da yin mulkin kasar.

Yayin da Atiku ya ke kalubalantar Tinubu, Mallam Nasir El-Rufai ya jaddada aniyar kawancen 'yan adawa na kifar gwamnatin APC domin dawo da Najeriya a turbar kwarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.